Nijeriya da ƙasashen Afirka sun haɗa kai domin ƙara haɓaka noman koko

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa Nijeriya tare da sauran ƙasashen Afirka masu noman koko sun cimma yarjejeniya kan ƙarfafa haɗin gwiwa domin bunƙasa sarrafa koko a cikin gida, ƙara yawan kuɗaɗen da manoma ke samu, da kuma faɗaɗa rabon da nahiyar Afirka ke samu daga kasuwar koko ta duniya.

ƙaramin Ministan Masana’antu, Sanata John Enoh, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na ɗ bayan kammala Taron ƙara Wa Koko ƙima (Kokoa ɓalue Addition Summit) da aka gudanar a Abuja.

A cewarsa, taron ya ƙare da amincewa da Sanarwar Abuja (Abuja Declaration), wadda ta zama wani tsari na bai ɗaya da aka ƙirƙira domin ƙarfafa sarrafa koko a cikin ƙasashen Afirka, tare da rage dogaro da fitar da ɗanyen ƙwayar koko zuwa ƙasashen waje.

Sanata Enoh ya bayyana cewa wannan mataki na da nufin gyara rashin daidaiton da aka daɗe ana gani a kasuwar koko ta duniya, inda ƙasashen Afirka ke samar da mafi yawan koko da ake nomawa a duniya, amma suke samun ƙaramin kaso ne kawai daga ribar masana’antar.

Ya ce, duk manomin koko da ya taɓa sayar da amfaninsa ƙasa da ƙimarsa ya san irin giɓin da ke tattare da harkar koko, kuma wannan taro an shirya shi ne domin cike wannan giɓi.

A cewarsa, tsawon shekaru ƙasashen Afirka suna fitar da ɗanyen koko zuwa ƙasashen waje, amma daga baya suna sake shigo da cakulan da sauran kayayyakin da aka sarrafa daga koko cikin tsadar da ba su da hannu wajen ƙayyade farashinsa.

Ministan ya ƙara da cewa, sabon tsarin zai bai wa Nijeriya da sauran maƙwabtanta damar sarrafawa, sanya tambarinsu da kuma ƙayyade farashin kayayyakin koko bisa muradunsu.

A ƙarƙashin Sanarwar Abuja, ƙasashen da suka halarci taron sun amince da haɗa kai wajen tsara manufofi kan cinikin koko na duniya, inganta ƙa’idojin samarwa da tsarin bibiyar asalin koko daga gona har zuwa kasuwa, tare da shirin cika sabbin ƙa’idojin kasuwancin ƙasa da ƙasa.

Daga cikin waɗannan sabbin ƙa’idoji akwai Dokar Tarayyar Turai kan Hana Sare Itatuwa (European Union Deforestation Regulation), wadda za ta fara aiki daga ranar 30 ga Disamban 2026. Dokar za ta wajabta wa masu fitar da koko da sauran amfanin gona su tabbatar da cewa kayayyakinsu ba su da alaƙa da sare dazuka kafin a ba su damar shiga kasuwannin Tarayyar Turai.

Sanata Enoh ya ce aiwatar da Sanarwar Abuja za ta amfani manoman koko, masu sarrafa koko da kuma ‘yan kasuwa, domin za ta ƙarfafa masana’antu a cikin gida, ƙara ƙarfin gasa tare da samar da shahararrun kayayyakin koko na Afirka da za su samu karɓuwa a duniya.

Ya ce, wannan sanarwa ta zo ne domin taimaka wa manomin da ke neman adalci wajen farashin amfaninsa, da mai masana’antar da ke faɗaɗa harkokinsa, da kuma ɗan kasuwar da ke son gina alamar kasuwanci da za ta yi fice a duniya.

Nijeriya na daga cikin manyan ƙasashen Afirka masu noman koko tare da Cote d’Iɓoire, Ghana da Kamaru. Sai dai kamar sauran ƙasashen da ke samar da koko, mafi yawan amfanin da take nomawa ana fitar da shi ne a matsayin ɗanyen koko, lamarin da ke rage ribar da ƙasar ke samu daga masana’antar cakulan da sauran kayayyakin da ake sarrafawa daga koko.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa taron Aara Wa Koko ƙima wani ɓangare ne na shirinta na bunƙasa sarrafa koko a cikin gida, inganta ƙa’idojin samar da kayayyaki, faɗaɗa kasuwannin fitar da kaya, da kuma bai wa ƙasashen Afirka damar samun kaso mai yawa daga kasuwar koko ta duniya wadda darajarta ta kai biliyoyin daloli.

By ukarofi

Leave a Reply