Duk da saukar hauhawar farashi, jihohi 19 da Abuja sun ci gaba da fuskantar tsaiko – NBS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Duk da cewa adadin hauhawar farashin kayayyaki a matakin ƙasa ya ɗan ragu a watan Yunin 2026, rahoton Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ya nuna cewa mazauna fiye da rabin jihohin Nijeriya na ci gaba da fama da matsanancin tashin farashi, inda jihohi 19 tare da Babban Birnin Tarayya Abuja, suka yi rajistar hauhawar farashi da ta zarce kashi 30 cikin ɗari.

Sabon rahoton Ma’aunin Farashin Mabuƙaci (CPI) da hukumar ta fitar ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ta sauka kaɗan daga kashi 15.93 cikin ɗari da aka samu a watan Mayu zuwa kashi 15.91 cikin ɗari a watan Yuni.

Sai dai nazarin alƙaluman jihohi ya nuna cewa jihohi 20 cikin 37 da suka haɗa da Abuja, wato kashi 54.1 cikin ɗari na jihohin ƙasar, sun samu hauhawar farashin kayayyaki da ta haura kashi 30 cikin ɗari a shekara.

Rahoton ya nuna akwai babban giɓi tsakanin matsakaicin adadin hauhawar farashi na ƙasa da abin da iyalai ke fuskanta a jihohi daban-daban. Ko da Jihar Imo, wadda ta fi kowacce jiha samun ƙarancin hauhawar farashi da kashi 19.47 cikin ɗari, har yanzu ta zarce matsakaicin adadin ƙasa da maki 3.56.

A cewar NBS, Jihar Neja ce ta fi kowacce jiha fama da hauhawar farashi a watan Yuni da kashi 42.23 cikin ɗari, sai Jihar Kogi da kashi 41.59 cikin ɗari, sannan Babban Birnin Tarayya, Abuja da kashi 39.91 cikin ɗari.

Sauran jihohin da suka yi rajistar hauhawar farashi sama da kashi 30 cikin ɗari sun haɗa da Jihar Kwara mai kashi 36.52 cikin ɗari, Plateau mai kashi 35.82 cikin ɗari, Sakkwato mai kashi 35.22 cikin ɗari, Benue mai kashi 35.06 cikin ɗari, Osun mai kashi 34.46 cikin ɗari, Yobe mai kashi 34.40 cikin ɗari, Kebbi mai kashi 34.07 cikin ɗari, Enugu mai kashi 34.00 cikin ɗari, Bauchi mai kashi 33.68 cikin ɗari, Gombe mai kashi 33.51 cikin ɗari, Oyo mai kashi 32.81 cikin ɗari, Lagos mai kashi 32.28 cikin ɗari, Akwa Ibom mai kashi 31.85 cikin ɗari, Adamawa mai kashi 31.82 cikin ɗari, Ekiti mai kashi 31.00 cikin ɗari, Taraba mai kashi 30.54 cikin ɗari da kuma Abia mai kashi 30.28 cikin ɗari.

A ɓangaren da suka fi samun ƙarancin hauhawar farashi kuwa, jihohin Imo, Ebonyi da Katsina ne suka zo kan gaba da kashi 19.47 cikin ɗari, kashi 20.79 cikin ɗari da kuma kashi 21.87 cikin ɗari bi da bi. Sauran sun haɗa da Ribas, Zamfara, Kaduna, Edo, Cross Riɓer, Delta, Borno, Kano, Anambra, Ondo, Ogun, Jigawa, Nasarawa da Bayelsa.

Sai dai NBS ta yi gargaɗin cewa bai kamata a ɗauki alƙaluman jihohi a matsayin ma’aunin kwatanta farashin kayayyaki kai tsaye ba, domin tsarin kashe kuɗi da nauyin kayayyaki da ayyuka ya bambanta daga jiha zuwa jiha. Rahoton ya kuma nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci na ci gaba da zama babban ƙalubale a jihohi da dama.

Jihar Kogi ce ta fi kowacce jiha yawan hauhawar farashin abinci da kashi 53.02 cikin ɗari, sai Jihar Neja da kashi 43.83 cikin ɗari, sannan Benuwe da kashi 40.83 cikin ɗari.

A Abuja kuwa, hauhawar farashin abinci ta kai kashi 40.20 cikin ɗari, yayin da Adamawa ta samu kashi 39.61 cikin ɗari, Osun kashi 39.56 cikin ɗari, Kwara kashi 39.00 cikin ɗari, Kebbi kashi 37.59 cikin ɗari, Sokoto kashi 37.01 cikin ɗari, Filato kashi 36.84 cikin ɗari da Yobe kashi 36.68 cikin ɗari.

Sauran jihohin da suka zarce kashi 30 cikin ɗari sun haɗa da Enugu, Gombe, Kaduna, Bayelsa, Jigawa, Ekiti, Akwa Ibom, Edo, Bauchi, Zamfara, Delta, Nasarawa, Kuros Riba da Oyo.

A ɓangaren da suka fi samun ƙarancin hauhawar farashin abinci kuma, Katsina ce ta zo farko da kashi 19.15 cikin ɗari, sai Ribas da kashi 23.81 cikin ɗari, sannan Imo da kashi 24.60 cikin ɗari.

A matakin ƙasa, hauhawar farashin abinci ta tsaya a kashi 17.52 cikin ɗari a watan Yuni idan aka kwatanta da kashi 25.41 cikin ɗari da aka samu a makamancin watan shekarar 2025.

Sai dai idan aka kwatanta da watan Mayu, hauhawar farashin abinci ta ƙaru daga kashi 2.98 cikin ɗari zuwa kashi 3.75 cikin ɗari.

NBS ta danganta wannan ƙarin da tashin farashin kayan abinci irin su ƙanƙanin kifi (crayfish), barkono sabo, tumatir, busasshen koren wake, garin doya, naman sa, ayaba, garin rogo, wake, garri, dankalin Turawa da kuma doya. Rahoton ya kuma nuna cewa Jihar Neja ce ta fi kowacce jiha samun ƙarin hauhawar farashi idan aka kwatanta da watan da ya gabata da kashi 11.65 cikin ɗari, sai Katsina da kashi 8.13 cikin ɗari, Kwara da kashi 7.52 cikin ɗari, Gombe da kashi 7.09 cikin ɗari, Kebbi da kashi 6.99 cikin ɗari, Filato da kashi 6.53 cikin ɗari, sannan Legas da kashi 6.37 cikin ɗari.

By ukarofi