Yadda APC ke amfana da rikicin NDC a Kano gabanin zaɓen 2027

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ƙara zage damtse wajen tattaunawa da manyan jiga-jigan adawa a Jihar Kano, yayin da jam’iyyar ke ƙoƙarin cin gajiyar rikicin cikin gida da ke addabar Nigeria Democratic Congress (NDC) gabanin babban zaɓen 2027.

Daga cikin waɗanda APC ke ƙoƙarin jawo hankalinsu akwai Sanata Rufa’i Sani Hanga mai wakiltar Kano ta Tsakiya, wanda shi ne kaɗai sanatan NDC mai ci daga jihar, da kuma tsohon Sanata Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ta Kudu.

Rahotanni sun nuna cewa Yilwatda ya gana da Sanata Hanga sau biyu cikin ‘yan kwanakin nan, ciki har da wata ganawa da ya je tare da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin. Haka kuma ya kai wata ziyara ta sirri gidan Sanata Kabiru Gaya a Abuja.

Masu nazarin siyasa na ganin irin waɗannan ziyarce-ziyarcen na cikin dabarun APC na jawo manyan ‘yan adawa zuwa cikinta, kamar yadda ta yi nasarar jawo tsohon Gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, a baya.

Yunkurin APC ya zo ne a daidai lokacin da Sanata Hanga ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda aka yi masa mu’amala a cikin tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar NDC.

An ruwaito cewa Hanga ya yi korafin cewa duk da goyon bayan da ya bai wa jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba a ba shi tikitin komawa Majalisar Dattawa ko kuma kujerar mataimakin gwamna ba.

Hanga ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ADC na da damar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 fiye da NDC, yana mai cewa tasirin NDC ya fi ƙarfi ne kawai a Kano, kuma ko a jihar ma yana ci gaba da raguwa.

Da yake mayar da martani a wata hira da gidan talabijin na DITV, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce korafin Hanga ya samo asali ne daga rashin samun tikitin takara.

Ya ce biyayya ga jam’iyya bai kamata ta dogara da samun mukami ba, tare da zargin Hanga da neman hujjar da zai yi amfani da ita wajen komawa APC.

Shi ma kakakin tafiyar Kwankwasiyya na biyu, Mansur Kurugu, ya ce ziyarce-ziyarcen siyasa abu ne na yau da kullum kuma ba za a ɗauke su a matsayin sauya sheƙa ba har sai an bayyana hakan a hukumance.

A cewarsa, tafiyar Kwankwasiyya tana da ƙarfi a matakin ƙasa, kuma ficewar wasu jiga-jigai ba za ta raunana ta ba.

Mataimakin Shugaban APC na Jihar Kano, Salisu Maje Gwangwazo, ya tabbatar da cewa ya gana da Sanata Hanga domin ƙarfafa masa gwiwar komawa jam’iyyar.

Wani jigo a APC da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ko da yake ba zai yiwu a ba Hanga ko Gaya tikitin takara kai tsaye ba, amma za a yi musu adalci idan suka shiga jam’iyyar.

Masanin kimiyyar siyasa kuma malamin jami’a, Dakta Kabiru Sa’idu Sufi, ya ce matakan da Yilwatda ke ɗauka na nuna cewa APC na ci gaba da aiwatar da dabarar haɗa manyan ‘yan adawa da tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya fara.

Ya ce idan har NDC ta rasa Sanata Hanga, hakan zai zama babban koma baya a siyasance da kuma ta fuskar ƙwarin gwiwa, domin wasu daga cikin magoya bayansa za su iya binsa.

Sai dai har zuwa yanzu, Sanata Hanga da Sanata Kabiru Gaya ba su bayyana a hukumance ko za su sauya sheƙa zuwa APC ba, duk da ci gaba da tattaunawar da suke yi da shugabannin jam’iyyar.

By ukarofi

Leave a Reply