Matuƙar INEC ba ta dogara da kanta ba ta fuskar kuɗi ba za ta ci gashin kanta ba, inji Amupitan

Spread the love

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar ba za ta iya gudanar da aikinta cikin cikakken ‘yanci ba muddin ba ta da cikakken ikon cin gashin kai ta fuskar harkokin kuɗi.

Amupitan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taro, inda ya jaddada cewa samun ‘yancin kuɗi na daga cikin muhimman sharuɗɗan da za su tabbatar da cikakken ‘yancin hukumar wajen gudanar da zaɓe ba tare da wani tasiri daga waje ba.

Ya bayyana cewa duk da cewa kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadi zaman kansa ga INEC, har yanzu akwai buƙatar ƙarfafa wannan matsayi ta hanyar bai wa hukumar cikakken iko kan yadda ake ware mata kuɗi da kuma yadda take gudanar da kasafin kuɗinta.

A cewarsa, wannan zai ƙara wa ‘yan ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki kwarin gwiwa kan gaskiya, adalci da sahihancin tsarin zaɓen Najeriya, tare da rage duk wani zargi na katsalandan a ayyukan hukumar.

Shugaban na INEC ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da za su ƙarfafa tsarin zaɓe, yana mai cewa samun cikakken ‘yancin gudanarwa da na kuɗi zai taimaka wajen tabbatar da sahihanci da amincin zaɓukan da za a gudanar nan gaba.

By Babaji

Leave a Reply