Yadda ‘yan sanda suka tilasta wa shugaban yaƙi da rashawa na Nijeriya bayar da cin hanci 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An daɗe ‘yan Nijeriya na kokawa game da ƙazancewar ayyukan rashawa a ma’aikatu da hukumomin gwamnati, kuma hukumar ‘yan sanda ta ƙasar na cikin waɗanda a kodayaushe ake nunawa, kan cewa jami’anta na yawan karɓar kuɗi daga al’umma sa’ilin da suke bakin aiki.

Amma an ce kwana dubu ta ɓarawo, kwana ɗaya kuma ta mai kaya.

A wannan karo shugaban hukumar yaƙi da rashawa da laifuka makamantan haka ICPC na Nijeriya, Musa Aliyu ne ya faɗa hannun wasu jami’an ‘yan sanda a birnin Abuja, waɗanda suka buƙace shi ya ba su kuɗi bayan zargin shi da laifin karya doka.

Tuni hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin har ma ta bayyana cewa ta fara ɗaukar mataki kan lamarin.

Shugaban na ICPC ya zo ofishin BBC da ke Abuja, inda aka tattauna da shi kan abubuwa daban-daban, inda ya yi ƙarin haske a kan yadda ‘yan sandan suka tursasa masa ba su cin hancin.

“A wata ranar Asabar ina tafiya a cikin mota, ni ne nake tuƙawa yayin da wasu ke bi na a baya, sai na isa bakin danjar bayar da hannu a mahaɗar Barneɗ,” inji Musa Aliyu.

“Lokacin da na tsaya sai wani ɗan sanda ya zo bakin ƙofar mota, sai na saukar da gilashi, sai ya ce na buɗe motata, sai na buɗe, sai ya shigo ciki.

“Bayan ya shiga sai ya fara min tambayoyi, ya ce na tsallake wutar bayar da hannu, na ce masa ban tsallake ba, domin na tsaya a lokacin da danja ta nuna ruwan ɗorawa”.

Aliyu ya ce a lokacin ma akwai wata motar a gaban tasa, wadda ɗan sandan bai je ya tuhume shi ba.

“Sai ya ce min na ba shi lasisin tuƙina, sai na fito da shi, ya ce na ba shi, sai na ba shi. Sai ya ce min zai kai ni kotu a kan na karya dokar hanya. Sai na ce masa mu je kotun.

“Bayan mun fara tafiya sai ya ce kai babban mutum ne, ba za ka so a ɓata maka lokaci ba, amma idan ma an je kotun za a yi maka tara ne ta Naira 52,000, sai ya ce min zan iya ba shi kuɗin ya je ya biya.

“Sai na buƙace shi ya ba ni lambar asusun ajiyarsa na banki domin na tura masa kuɗin, sai ya ƙi, ya ce min akwai wurin POS gaba kaɗan, sai muka tafi wurin POS, na cire kuɗi 53 na ba shi sannan na biya mai POS naira 1,000.

“Bayan nan sai ya buƙace ni na ba shi kuɗin mota da zai je kotu ya biya kuɗin, sai na ba shi 2,000, amma ya ce sun yi kaɗan, sai na ƙara masa 3,000.

“Daga nan sai na sake mayar da shi inda na ɗauko shi. Bayan na ajiye shi sai ya hau tasi, na bi tasin amma a ƙarshe sun ɓace min,” a cewar shugaban na ICPC.

Daga nan ne shugaban na hukumar ICPC ya kai rahoto ga jami’an tsaro.

Musa Aliyu ya ce a jimilla ya bai wa jami’in ɗan sandan naira 57,000.

“Abin da ya sa na yi hakan shi ne domin na fahimci yadda ake irin wannan abu domin mu kare faruwar hakan”.

A ranar Litinin rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Abuja, babban birnin ƙasar ta kira wani taron manema labarai inda ta bayyana cewa ta fara bincike game da wasu ‘yan sanda da suka tursasa wa shugaban ICPC ba su kuɗi ba ta hanyar da ta dace ba.

A lokacin da yake magana, kwamishinan ‘yansandan yankin Abuja Ahmed Sanusi ya tabbatar da cewa lallai wasu jami’an ‘yan sanda sun karɓi kuɗi a hannun shugaban ICPC Musa Aliyu.

Ya ce: “Sun tatsi shugaban ICPC kuɗi naira 53,000 bayan sun kai shi wajen mai sana’ar POS, inda suka karɓi kuɗin suka raba a tsakaninsu.

Kwamishinan ya ce bincikensu ya gano cewa wasu ‘yan sanda sun kafa gungu na masu tatsar kuɗi daga al’umma, inda suke zuwa suna yin aiki ba bisa kan ƙa’ida ba.

“Mun kama dukkansu, za mu tabbatar an musu hukunci mai tsanani, wadanda suka cancanci a kore su, za mu tabbatar an kore su,” inji CP Sanusi.

Cin hanci da rashawa gagarumar matsala ce da ke addabar ƙasashen duniya tare da haifar da matsalolin tattalin arziki.

ƙasashen duniya da dama na fama da matsalar ta cin hanci da rashawa, wani abu da ke kawo tarnaƙi ga ci gaban ƙasashen.

A rahotonta na shekara ta 2026, ƙungiyar Transperancy International mai yaƙi da cin hanci da rashawa a duniya ta ce duk da ci gaban da aka samu a yaƙi da cin hanci da rashawa a duniya, matsalar ta ci gaba da kasancewa babbar barazana ga ci gaban ƙasashen duniya.

A cikin jerin da ta fitar Nijeriya ta kare kambinta a matsayin ta 37 a cikin ƙasashen duniya masu fama da matsalar cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2025.

Rahoton ya nuna cewa a tsawon shekara uku Nijeriya ta kasance tana da maki 26 cikin 100.

Hakan ya sanya Nijeriya a matsayi na 142 daga cikin ƙasashe 182 da ƙungiyar ta yi nazari a kai.

Rahoton hukumar ya nuna cewa tun daga shekara ta 2022, matsalar cin hanci ta ragu da maki biyu a Nijeriya.

A shekarar 2025 Nijeriya ta samu maki 26 daidai da makin da ta samu a 2024, sama da abin da ta samu a 2023, lokacin da take da maki 25.

An haifi Dr. Musa Adamu Aliyu a ranar 27 ga Disamban 1977 a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ne da ke a jihar Jigawa a arewa maso yammacin ƙasar.

Dr. Aliyu ya yi Makarantar Firamare ta Central Primary School da ke Birnin Kudu tsakanin 1983 zuwa 1989.

Daga nan ya yi sakandare a Government College Bauchi daga 1990 zuwa 1995, kafin ya ci gaba da karatu a Kano State College of Arts, Science and Remedial Studies tsakanin 1996 da 1997.

Ya samu digirin farko a fannin shari’a (LLB) daga Jami’ar Bayero da ke Kano tsakanin 1998 zuwa 2003, sannan ya halarci Makarantar Horar da Lauyoyi ta Kasa da ke Bwari a Abuja daga 2003 zuwa 2004.

Ya kuma samu digiri na biyu (LL.M) daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2011. A shekarar 2019 kuma ya kammala digirin digirgir (PhD) a fannin shari’a daga Universiti Utara Malaysia.

A ranar 12 ga Oktoban 2023 ne Alƙalin Alƙalan Nijeriya a lokacin, Olukayode Ariwoola, ya ba shi lambar girma ta Senior Advocate of Nigeria (SAN) inda aka rantsar da shi a ranar 27 ga Nuwamban 2023.

Kafin zama shugaban ICPC, Dr. Aliyu ya yi aiki a matsayin lauya a cibiyar lauyoyi daban-daban.

Ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Shari’a na jihar Jigawa daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya naɗa shi shugaban hukumar ICPC ne a ranar 17 ga Oktoban 2023, kafin Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin nasa, inda aka rantsar da shi a ranar 13 ga Disamban 2023.

By ukarofi

Leave a Reply