Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Isaac Fayose ya buƙaci ɗan’uwansa, tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, da ya ƙi karɓar naɗin da aka yi masa a matsayin Shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), yana mai cewa muƙamin bai dace da irin matsayinsa na siyasa ba.
Isaac ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Litinin, bayan Fadar Shugaban ƙasa ta sanar da naɗin Ayo Fayose tare da wasu mutum 25 a shugabancin hukumomi da kwamitocin gwamnatin tarayya guda 10.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Fayose a matsayin Shugaban Hukumar REA, tare da Ahmadu Abubakar da Ilyasu Ibrahim Makinta a matsayin daraktoci marasa zartarwa. Haka kuma, an ci gaba da riƙe Abba Abubakar Aliyu a matsayin Darakta Janar na hukumar, tare da sauran daraktocin zartarwa uku.
Da yake mayar da martani, Isaac Fayose ya ce ɗan’uwansa ya cancanci muƙami mafi girma a matakin ƙasa.
Ya ce, “An ba wa ɗan’uwana shugabancin wata hukuma ce kawai, ba minista ba, ba jakada ba,” yana mai cewa wannan naɗi bai dace da matsayin siyasar tsohon gwamnan ba.
Ya kuma kwatanta naɗin da aka yi wa tsohon hadimin shugaban ƙasa, Reno Omokri, yana ikirarin cewa an naɗa shi jakada, yayin da aka bai wa ɗan’uwansa muƙami da ya fi ƙanƙanta.
Isaac ya kuma yi zargin cewa naɗin na da alaƙa da ziyarar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya kai masa kwanan nan.
A cewarsa, “Sun ba wa ɗan’uwana wannan muƙami ne saboda Peter Obi ya zo ya ziyarce ni. Sun ce dole su shiga wannan iyali.”
Isaac Fayose ya tunatar da cewa tsohon gwamnan ya sha bayyana cewa ba zai sake neman ko karɓar wani muƙamin gwamnati ba bayan ya bar ofis, domin yana son mayar da hankali kan harkokinsa na kasuwanci.
Ya ƙara da cewa Ayo Fayose ya tara dukiyarsa tun kafin ya shiga siyasa, don haka ba ya buƙatar wani sabon muƙamin gwamnati.
Isaac ya bayyana shugabancin Hukumar REA a matsayin “kyautar Girka” (Greek gift), yana mai tambayar dalilin da ya sa aka jira shekaru da dama bayan barin mulki kafin a ba shi wannan naɗi.
Da yake magana kai tsaye ga ɗan’uwansa, Isaac ya ce, “Ka fi ƙarfin wannan muƙami. Ka ba ɗanka wannan naɗin.”
A ƙarshe, ya sake bayyana kwarin gwiwarsa cewa ‘yan adawa na da damar samun nasara a zaɓen shekarar 2027, yana mai bayyana fatansa cewa za a gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.
