Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken ayyukan hukuamr bogi ta bunƙasa zuba hannun jari ta fadar shugaban ƙasa (PFIPC), ta gayyaci mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro NSA), Nuhu Ribadu, domin ya bayyana matakan da ofishinsa ya ɗauka bayan tabbatar da cewa hukumar ba ta cikin hukumomin gwamnatin tarayya.
Kwamitin ya kuma umarci Ministan Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta gurfana da kanta a gaban kwamitin, bayan bayanan da Sakataren Dindindin na ma’aikatar, Dunoma Ahmed, ya gabatar a ranar Talata.
Kwamitin a ƙarƙashin jagorancin Yusuf Gagdi (APC, Plateau), na binciken yadda ake zargin PFIPC ta riƙa gabatar da kanta a matsayin hukuma ta fadar shugaban ƙasa duk da cewa ta bogi ce.
‘Yan majalisar na kuma binciken zarge-zargen cewa kungiyar ta rika amfani da sunan Fadar Shugaban ƙasa wajen tuntuɓar hukumomin gwamnati da jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje, har ma aka ware mata kasafi a cikin kuɗin shekarar 2026.
Da yake ba da magana a gaban kwamitin, Mista Ahmed ya ce Ma’aikatar Harkokin Waje ba ta taɓa amincewa da PFIPC a matsayin hukuma ba, kuma ba ta da wata hulɗa a hukumance da ita.
Hakazalika ya ce, mutumin da ke iƙirarin shi ne darakta-janar na hukumar, Adeniyi Adeyemi, ba sananne ba ne a wurin gwamnatin tarayya.
A cewarsa, Mista Adeyemi ya rubuta wa ma’aikatar sau uku — a ranakun 26 ga Yuni, 2025, 5 ga Agusta, 2025 da 5 ga Yuni, 2026 — yana neman haɗin gwuiwa da amincewa domin shirya wani taron zuba hannun jari na duniya a Nijeriya.
Ahmed ya ce Adeyemi ya bayyana kansa a matsayin darakta-janar na kwamitin ba da shawara ga shugaban ƙasa kan zuba jari (PEAC) da kuma kwamitin bunƙasa zuba hannun jari na fadar shugaban ƙasa (PFIPC).
Sai dai ya ce ma’aikatar ta yi watsi da dukkan buƙatu ukun bayan gudanar da bincike, inda ta gano rashin daidaito a takardun da aka gabatar tare da samun shakku kan sahihancin hukumar da kuma shugabancinta.
Ya bayyana cewa daga bisani ma’aikatar ta rubuta wa ofishin mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) a ranar 16 ga Oktoba, 2025, tana neman ƙarin bayani kan matsayin Mista Adeyemi.
A cewarsa, ONSA ta mayar da martani a ranar 26 ga Nuwambar 2025 bayan ta tuntubi Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) da kuma Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, inda ta tabbatar da cewa ba ta da masaniyar wanzuwar Adeyemi a matsayin shugaban kowacce hukuma ta gwamnatin tarayya.
Ahmed ya ƙara da cewa ma’aikatar ba ta taɓa shiga wata hulɗar diflomasiyya da PFIPC ba, kuma ba taɓa taimaka mata wajen haɗa ta da masu zuba jari ko ƙungiyoyi na duniya ba. Sannan ba ta umarci ofisoshin jakadancin Nijeriya da ke ƙasashen waje su yi hulɗa da Adeyemi ba.
Ya kuma ce ba a rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU), yarjejeniyar zuba jari ko wata yarjejeniyar ta duniya ba da cibiyar PFIPC ba, kuma bayan wasiƙun da aka gabatar wa kwamitin, ma’aikatar ba ta da wani ƙarin bayani ko takardu kan cibiyar.
Da yake martani ga shaidar, shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya nuna damuwa cewa duk da ONSA ta tabbatar tun a watan Nuwamban 2025 cewa PFIPC ba hukuma ba ce ta gwamnati, har yanzu akwai tambayoyi kan matakan da aka ɗauka bayan samun wannan tabbaci.
Saboda haka, kwamitin ya gayyaci Ribado ya bayyana a gabansa a ranar Alhamis da ƙarfe 12:00 na rana, domin ya yi bayani kan matakan da ofishinsa ya dauka bayan gano cewa PFIPC hukumar ce ta bogi.
Gagdi ya ce kwamitin na son jin daga bakin mashawarcin shugaban ƙasar kan irin matakan da ta ɗauka bayan ma’aikatar harkokin waje ta nuna shakkunta kan sahihancin hukumar.
Ya ce da zarar Ribado ta tabbatar cewa PFIPC ba hukuma ce ta gwamnati ba, “ya kamata ta dauki matakan da suka dace,” yana mai cewa kwamitin zai tantance ko an yi abin da ya kamata domin dakatar da ci gaba da ayyukan ƙungiyar.
Wannan sabon bayani ya ƙara yawan hukumomin gwamnati da suka nesanta kansu da hukumar PFIPC.
A ranar Litinin, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya shaida wa kwamitin cewa asusun ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje guda biyu da ke da alaƙa da PFIPC ba su taɓa yin wata mu’amala ba tun bayan buɗe su.
Haka kuma, shugabar ma’aikatar gwamnatin tarayya, Didi Walson-Jack, ta bayyana cewa ba a taɓa kafa hukumar PFIPC bisa ƙa’idojin da ake bi wajen ƙirƙirar hukumomin gwamnatin tarayya ba, kuma ofishinta bai amince da kafuwar hukumar ko kuma naɗa Adeniyi Adeyemi a matsayin darakta-janar ba.
