
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta kama Shugaban Ƙungiyar Matasan Borno ta Kudu (BOSYA), Samaila Ibrahim Kaigama bayan wasu kalamai da ya yi a hirar talabijin, inda ya yi zargin cewa an biya mayaƙan Boko Haram da ‘yan bindiga kuɗaɗen fansa.
Rahotanni sun bayyana cewa, an garzaya da Kaigama zuwa ofishin DSS ne jim-kaɗan bayan kammala hirar, wadda aka gudanar da ita a tashar Channels, inda ya yi tsokaci akan ƙalubalen da arewacin Nijeriya ke fuskanta kuma ya yi iƙirari akan batun sako mutanen da aka sace a Borno.
A yayin hirar, Kaigama ya zargi Gwamnatin Tarayya da biyan Naira biliyan 5 ga mayaƙan Boko Haram domin su sako mata da yaran da aka yi garkuwa da su a garin Ngoshe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Haka kuma, ya yi zargin cewa Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu na daga cikin waɗanda suka jagoranci bayar da kuɗin, inda biliyan N1.9 ne kaɗai aka bayar, sauran kuma bai san yadda aka yi ba.
Kazalika, ya ce yana da hujjar da ke nuna cewa an biya mayaƙan Boko Haram da ‘yan bindiga, yana mai zargin hukumomi ne suka yi ta ƙoƙarin yin rufa-rufa domin kada ‘yan jarida su sani.
Saidai, gwamnatin Borno a nata ɓangaren, ta yi watsi da dukkan zarge-zargen nasa, inda ta ce babu wani kuɗin fansa da aka biya yayin sako mutanen da aka sacen.
A cewar hukumominta, an ceto mata da yaran ne yayin wani atisaye ta amfani da bayanan sirri daga jami’an tsaro, wanda sojoji da DSS suka jagoranta.
