Ɗaya daga cikinmu ba ya iya biyan kuɗin makarantar ‘ya’yansa, inji ɗan Majalisar Wakilai kan zargin biyan su sama da kima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani ɗan Majalisar Wakilai mai suna Chunedu Obika, ya ƙalubalanci batun da ake yaɗawa cewa ana biyan ‘yan majalisar dokokin ƙasa sama da kima, yana mai cewa kwanan nan ya samu labarin cewa ɗaya daga cikin takwarorinsu ya fuskanci ƙalubale wajen samar da kuɗin karatun ‘yarsa Naira 700,000.

Obika, wanda ke wakiltar AMAC/Bwari a Majalisar, ya ce shi ne wanda ya tallafa wa ɗan majalisar biyan kuɗin makarantar kimanin wasannin biyu da suka gabata.

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da KAA Truths da aka wallafa a ranar Alhamis yayin amsa tambaya akan cece-kucen al’umma kan biya da walwalar ‘ya’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

A cewarsa, wannan al’amari ya nuna cewa, ba dukkanin ‘yan majalisa ba ne ke samun walwalar kuɗaɗe kamar yadda al’umma suke zato.

Ya bayyana cewa, da dama mutane suna ƙasa fahimtar shuru da wasu ‘yan majalisa suke yi, yana mai tirjewa akan ba suna yin hakan ba ne don an biya su, saidai sun ɗauki matakin ne don ba sa amfana a karan kansu.

Ya ƙara da cewa, albashi da alawus ɗin ‘yan majalisa ba ɓoyayye ba ne a wajen al’umma, yana mai kira ga jama’a da su riƙa amfani da sahihan labarai a madadin dogaro da zato.

By Babaji

Leave a Reply