Mun ɗauka rasuwa za mu yi, inji ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin Enugu Air da suka tsira

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani fasinjan jirgin Enugu Air da ya yi saukar gaggawa a filin jiragen saman Benin, ya bayyana yadda suka tsinci kansu a cikin halin firgici yayin da jirgin nasu ya goce daga ainihin titinsa.

Ya yi zargin cewa jami’an gudanarwa sun gaza kula da al’amarin, inda ya ce har yanzu kamfanin bai bayar da haƙuri a gare su ba a hukumance.

Fasinjan, wanda sanannen na siyasa ne a Jihar Edo, ya magantu ne bisa neman a sakaye sunansa, ya bayyana cewa, jirgin ya taso ne daga filin Murtala Mohammed sashe na 2 (MM2) da misalin ƙarfe 2:06 na ranar Alhamis.

Bayan wani direban jirgin mai suna Kyaftin Ladi ya sanar da fasinjoji cewa jirgin zai yi tsawon tafiya zuwa Benin ta minti 35, yana mai gargaɗin cewa akwai yiwuwar a samu tangarɗa saboda yanayin sararin samaniya.

A cewarsa, an fara tafiya cikin lumana, inda jim-kaɗan bayan haka ne aka sanar da su cewa ba za a ba su makari ba saboda tafiyar ba ta tsawo har sai sun isa inda suka nufa. Ba da jimawa ba ne wani direban ya sanar da cewa jirgin na dab da sauka.

Ya bayyana cewa, jirgin ya sauka ne yayin da ake tsaka mamakon ruwan sama, saidai ya gaza tsayawa, wanda a lokacin ne ya karci wani sashen na gefen titin, lamarin da ya sa ɗaya daga cikin tayoyinsa ya yi dameji.

A yayin haka ne ya zargi cewa fasinjoji sun taru a hanyar fita ta gaggawa amma ba su san yana su yi ba saboda gazawar aikin jami’an jirgin na ba su kulawa da kuma rashin isar ‘yan kwana-kwana zuwa wajen akan lokacin, lamarin da ya sa suka shiga ɗimuwa.

By Babaji

Leave a Reply