‘Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma da kashe jami’an tsaro a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun yi awon-gaba da Shugaban Ƙaramar Hukumar Bunguɗu ta Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar Bunguɗu, bayan ƙaddamar wani mummunan hari da dare a gidansa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro guda uku.

An ruwaito cewa maharan sun kai farmakin ne acikin daren Alhamis wayewar Juma’a, inda suka farmaki gidan ciyaman ɗin da ke yankin Zango, ƙasa da kilomita 20 daga Gusau, Babban Birnin jihar.

A yayin harin, ‘yan bindigar sun nuna fin ƙarfi ga jami’an da ke gadin gidan, inda suka halaka ‘yan sanda da ‘yan bijilante biyu-biyu kafin suka yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar da iyalansa.

Yunƙurin daƙile harin daga ɓangaren jami’an tsaro bai yi nasara ba kasancewar ‘yan bindigar sun je da makamai masu ƙarfi da adadi mai yawa, lamarin da ya sa suka tsere da Hon. Umar.

Wata majiya ta ce, an sace shi ne tare da matarsa da ‘ya’yansu, saidai jami’an, a lokacin da suke musayar wuta da ‘yan bindigar sun yi nasarar ceto yara huɗu ko biyar kafin maharan su tsere.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a san halin da iyalin nasa take ciki ba duk ƙoƙarin ceto ta daga hannun ‘yan bindigar, sannan ba a hi ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar ba.

By Babaji

Leave a Reply