Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Al’ummar ƙaramar hukumar Bungudu sun shiga cikin baƙin ciki a daren Juma’a, bayan wani hari da yan bindiga suka kai wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro 4, da raunata wasu da dama, tare da sace shugaban ƙaramar hukumar Bungudu.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:40 na dare a ranar Juma’a, kamar yadda rahotannin daga al’umma suka bayyana.
Majiyoyi sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce yan bindigar sun yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Bungudu, Hon. Nura Umar Abdullahi, a lokacin harin.
An kuma yi garkuwa da wasu fararen hula guda biyu tare da shi. Sun haɗa da Halliru Ahmad Soja, ma’aikaci a asibitin ƙwararru na tarayya da ke Gusau, da kuma Hussaini Naira, wani matashi ɗan kasuwa wanda ke gudanar da kasuwancin POS da kiran waya.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a san inda suke ba.
Harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro guda huɗu da ake cewa sun je ɗaukar mataki kan lamarin.
Sunayen waɗanda suka mutu su ne: Inspekta Basiru Lawal, Kofur Hamza Muhammad, ADC din shugaban ƙaramar hukumar, da membobin ‘yan banga biyu: Ibrahim Ba’are da wani memba na ‘yan banga.
Har ila yau, Alh. Bello Umar Abdullahi (ST), tsohon ma’ajin ma’aikatar kudi ta Jihar Zamfara, ya jikkata a harin. A halin yanzu yana samun magani a asibiti saboda raunukan da ya samu.
A cikin wata sanarwa ta al’umma na jaje, sun bayyana baƙin cikinsu kan lamarin.
“Muna rokon Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya kuma ba iyalansu hakurin jure wannan babbar asara,” in ji sanarwar. “Ga waɗanda suka jikkata, muna addu’ar Allah ya ba su lafiya cikin gaggawa.”
Mazauna yankin sun kuma roƙi jama’a da su kara yawan addu’a domin a ceto waɗanda aka sace lafiya, da kuma neman zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
“Muna rokon Allah madaukakin sarki ya ceto waɗanda aka yi garkuwa da su lafiya, ya kuma dawo da zaman lafiya da tsaro a Bungudu, Jihar Zamfara, da ma ƙasar baki daya,” in ji sanarwar.
Ƙaramar hukumar Bungudu dake Jihar Zamfara na fama da hare-haren yan bindiga a ‘yan shekarun nan. Sace-sacen neman kuɗin fansa da kai hari kan jami’an gwamnati sun zama babbar matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro na Jihar Zamfara ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma ba game da harin.
Ƙoƙarin ɗan jaridar mu na tuntubar rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara domin jin ta bakinsu bai yi nasara ba.
