Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An gudanar da shirin dashen bishiyoyi 16,000 mai taken “Dikko Green”, a titunan WTC, Filin Polo da kuma Kofar Sauri zuwa Shinkafi, cikin garin Katsina.
Da yake gabatar da jawabinsa, mai bai wa gwamna shawara kan harkokin sauyin yanayi, Prof. Muhammad Al’amin, ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci ƙaddamar da dashen bishiyoyi 16,000 da gwamnatin Jihar Katsina ta samar ƙarƙashin shirin “Dikko Green.”
Hakazalika, ya bayyana cewa wannan na daga cikin yunƙurin gwamnatin Jihar Katsina na magance matsalar ɗumamar yanayi.
Shi ya sa ta ga ya dace a dasa bishiyoyi 16,000 domin samar da wadatacciyar iska da kuma rage zafin da ake fuskanta a Jihar Katsina ya ce.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude , ya bayyana farin cikinsa kan wannan shiri na gwamnatin Jihar Katsina tare da gode wa gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, bisa tunanin samar da wannan shiri ga al’umma.
Shi ma da yake gabatar da jawabinsa, mataimakin gwamna na musamman kan harkokin kafafen sadarwa, Mustapha Samaila Ingawa, ya yi kira ga al’umma da su zama masu kula da bishiyoyin da aka dasa, domin gwamnati tana ƙoƙarin kiyaye muhalli da kare al’umma daga illar ɗumamar yanayi. Don haka ya ce mutane su ba da gudummawarsu domin ganin gwamnati ta cimma burinta.
Shima mai taimakawa gwamna kan sauyin yanayi, Hon. Sulaiman Ribado, ya ce wannan shirin dashen bishiyoyi da gwamnatin jihar Katsina ke aiwatarwa a cikin birnin Katsina, musamman a sabbin titunan cikin gari, zai taimaka wajen samar da yanayi mai kyau ga al’umma, musamman ganin yadda aka cire wasu tsofaffin bishiyoyi domin maye gurbinsu da sababbi.
Ya yi kira ga al’umma da su shiga cikin aikin kula da waɗannan bishiyoyi domin su samu kulawa har su girma, al’umma kuma su amfana da su. Ya ce hakan zai taimaka wajen samar da kyakkyawan yanayi tare da rage matsaloli da dama.
A nasa jawabin, wakilin magajin garin Katsina, Alh. Audu Iliyasu Wakili Kudu, ya yaba da wannan shiri na dashen bishiyoyi, yana mai cewa zai taimaka wajen yaƙi da kwararowar hamada, magance zaizayar ƙasa da kuma samar da wadatacciyar iska ga al’umma. Ya ce kowa ya san muhimmancin dashen bishiyoyi da alherin da yake tattare da shi.
A madadin al’ummar garin Katsina, ya gode wa wannan hukuma da kuma gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa bisa kawo wannan shiri domin samar da yanayi mai kyau ga al’umma.
