Daga USMAN KAROFI
Hukumomin tsaro na ƙasar Morocco sun fara gudanar da bincike kan zargin satar fiye da dala 1,200 daga ɗakunan ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, yayin da suke ci gaba da shirye-shiryen shiga gasar kofin nahiyar Afirka ta mata (WAFCON) ta 2026. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya fito fili ne bayan ‘yar wasan gaba, Esther Okoronkwo, ta bayyana abin da ya faru a shafinta na Snapchat.
‘Yan wasan suna sauka ne a otal ɗin Marriott da ke birnin Casablanca, inda ake zargin ma’aikatan tsaftar otal ɗin da samun damar shiga ɗakunansu lokacin da tawagar ta fita atisaye. Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda sun fara duba faifan bidiyon kyamarorin tsaro (CCTV) domin gano duk wanda ya shiga ɗakunan a lokacin da ake zargin an aikata satar.
Rahotanni sun ce Esther Okoronkwo ce ta fi fuskantar asara, inda aka sace mata dala 700. Haka kuma, kyaftin ɗin ƙungiyar Rasheedat Ajibade ta rasa dala 200, Joy Omewa ta rasa dala 120, yayin da Osinachi Ohale da Halimatu Ayinde suka ce an sace musu dala 100 kowacce. Jimillar kuɗin da aka sace daga ‘yan wasan ta kai dala 1,220, kwatankwacin kusan naira miliyan 1.7.
Duk da wannan lamari da ya tayar da hankali, hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) tare da mai horas da ƙungiyar, Justine Madugu, na ƙoƙarin tabbatar da cewa hankalin ‘yan wasan bai karkata daga shirye-shiryen gasar ba. Super Falcons za ta fara wasanninta na rukuni na C a birnin Rabat da wasan farko da Malawi, kafin ta kara da Zambia da Masar a ci gaba da gasar.
