Miyetti Allah ta koka kan halin da Fulani ke ciki a Oyo

Daga jaridar Manhaja

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na Jihar Oyo Ibrahim Abubakar Jiji, ya yi korafin halin da ake ciki mambobinsu na zaman dar-dar ne a jihar biyo bayan harin da wasu matasa da ba a san ko su wane ne ba suka kai wa Sarkin Fulani Salihu Abdulkadir a yankin Igangan, a Juma’ar da ta gabata.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Jihar Ondo ta bai wa Fulani makiyaya a jihar wa’adin kwana 7 a kan su fice mata daga dazuzzukanta.

Gwamnatin Jihar Ondo ta ci gaba da kallon matakin da ta dauka a matsayin abin da ya dace, ta ce hakki ne a kanta tabbatar da tsaron ‘yan jihar.

Sai dai kungiyar Miyetti Allah reshen Jihar Oyo ta nuna damuwarta dangane da irin barazanar da ta ce ‘ya’yanta na fuskanta a jihar.

Sa’ilin da yake ganawa da manema labarai a karshen makon da ya gabata a Ibadan, Alhaji Jiji ya bukaci gwamnatin jihar Oyo da ta tarayya da su bada umarnin a kamo wani mai suna Chief Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho bisa zargin harin da aka kai.

A cewar Alhaji Jiji sakamakon abin da ya faru, yanzu Fulani makiyaya zaman zullumi suke yi a jihar sannan wasunsu da dama sun bar gidajensu do neman mafaka a wasu wurare.

Yayin da ya yi kira ga Fulani da Yarabawa a yankin da a yi zaman lafiya da juna, shugaban kungiyar ya ce: “Tun da gwamnati ita ce gaba da kowa, ya kamata gwamnatin jihar da ta tarayya su kawo dauki tare da tabbatar da tsaron mazaunan yankin.”

Ya ci gaba da cewa, “Ya zama wajibi mu koyi zama lafiya da junanmu. Dukkanmu ‘yan Nijeriya ne. Muna godiya da kuma kaunar gwamnan Jihar Oyo, Engr. Seyi Makinde bisa fadin gaskiya. Akwai bukatar mu hada hannu domin tabbatar da al’uma mai lumana. Mutanenmu ba su ji dadi ba kuma da yawansu a tsorace suke. Wasunsu ma sun yi kaura don neman mafaka.”