A yanzu Gwamnatin Abba Kabir ce ke bin ‘yan Kannywood bashi – Darakta Ismael Khalil

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano 

A yayin da ‘yan masana’antar Kannywood suka shiga cikin harka siyasa tare da samar da ƙungiyoyi domin su ma a dama da su, ƙungiyar  Kannywood Awareness Network Abba Gida-Gida, ƙarƙashin shugabancin Darakta Ismael Khalil Ja’en tana ƙoƙarin shirya wani babban taro domin nuna goyon bayan su ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano don sake zabar sa a karo na biyu.

Wakilin mu ya tattauna da Darakta Ismael Khalil Ja’en domin jin manufar su ta shiga siyasa a matsayin su na ‘yan Kannywood da kuma samar da ƙungiyoyi Kannywood Awareness Network For Abba Gida’Gida. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Kuna daga cikin ‘yan Kannywood da kuka shiga harkar siyasa har ma ka sanar da ƙungiyar Kannywood Awareness Network For Abba Gida’Gida. Muna so ka yi wa masu karatu bayani a game da manufar ku da kuma abin da kuke so ku cimma a game da ƙungiyar.

ISMAEL KHALIL JA’EEN: To ita wannan ƙungiya ta Kannywood Awareness Network For Abba Gida’Gida, ba sabuwar ƙungiya ba ce, domin ta daɗe tana tallata ayyukan Maigirma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, don ta kai kusan shekaru huɗu, amma farko ba da wannan sunan ta fara ba, a farko sunan ta Kwankwasawan Kannywood, tun lokacin da Gwamna yana NNPP. To da ya fita daga jam’iyyar sai muka bi shi APC , wannan ya sa muka sauya sunan ƙungiyar.

Ita wannan ƙungiya tana tallata ayyukan Maigirma Gwamnan Kano kuma ƙungiya ce da ta haɗo kan mutanen masana’antar Kannywood jarumai furodusa darakta da sauran su. Kuma wannan ƙungiya mun tsaya ne domin nemar wa ‘yan cikin Kannywood makoma a cikin wannan tafiya ta gwamnati. Duba da cewar wasu suna tallata ayyukan Maigirma Gwamna amma ba su da hanyar da zai san da su da kuma yadda za su mori gwamnati saboda ba su da hanya ko wata kafar da za a ganin su.

To samar da wannan ƙungiya sai aka matsowa da mutane kusa, tun da wannan ƙungiya tana tare da jagorori na gwamnati. Misali akwai Abba El-Mustapha Shugaban Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano, akwai Sani Musa Danja yana cikin gwamnati da Aina’u Ade Mataimakiyar Gwamna a kan harkar Kannywood da kwamishinoni da muke da alaƙa da su irin su dakta Gaddabi da suke kasance iyaye na wannan ƙungiya, don haka duk wani abu idan ya taso idan ana son a taimaki wannan masana’antar yana biyowa ta wannan ƙungiya domin a isar da sakon taimakekeni ga ‘yan Kannywood.

To masana’antar Kannywood me ta fi buƙata gwamnati ta yi mata a yanzu?

To Alhamdulillah, duk abin da za ka bu1ata ga gwamnati ai bai wuce ilimi ba. To mu ‘yan fim a wannan gwamnati babu abin da za mu ce sai sam barka , domin an samar mana da makaranta ta fim a Tiga wanda ita wannan makarantar an samar da ita ne tun lokacin Kwankwaso yana gwamna, amma ba ta fara aiki ba har ya bar gwamnati, shi kuma Ganduje da ya zo bai ci gaba da ita ba, sai da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zo ta fara aiki, kuma alhamdulillah a wannan dawo da ita din an yi horo an yaye ɗalibai  kusan sama da ɗari biyar a wannan makarantar kuma gwamnati ta ba su kayan aiki da kuɗaɗen tallafi. Don haka duk abin da za ka bai wa ɗan Adam bai wuce ilimi ba.

Sau da dama idan aka bayar da horo aka bada tallafi ga ƙungiyoyi a kan samu wasu su sayar a maimakon su yi amfani da shi. Ko ka gamsu da cin gajiyar da ƙungiyar ku ta y ga tallafin da gwamna ya bayar wajen yin amfani da shi?

To Gaskiya na gamsu, domin ba zan manta ba yau ko wata guda ba a yi ba na je wani biki na ga wata tana ɗaukar hoto, hankalina yana kaiwa kanta sai na ga tana daga cikin ɗaliban da aka yaye, kuma wannan kyamara da gwamna ya raba mana da ita take wannan aikin. Kuma take nuna mini cewar  ta yi aiki da ita mai yawa. Wannan ya nuna da yawan mutane suna amfani da kayan da aka ba su.

A yanzu kenan kun wadatu da abin da kuka samu daga gwamnati ko kuna buƙatar ƙari?

Ai a yanzu ne ma muke son ƙari ta fannin ilimi da kuma jari domin horon da aka ba mu ya sa mun kara fahimtar harkar tana buƙatar ilimi sosai da kuma ƙarfin jari, don haka wannan ilimi muna son a ɗaga darajar sa, misali daga horas da mu da aka yi, muna son mu samu ƙarin tallafin karatu a jami’o’i saboda duk abin da za ka samu zai ƙare amma ilimi ba ya 1arewa kuma da ilimi ne za ka kai duk wani mataki da kake so ka kai.

To a yanzu ta wacce hanyar za ku saka wa gwamnati da irin wannan tagomashi da kuka samu?

To alhamdulillah mu yanzu ‘yan masana’antar Kannywood Maigirma Gwamna Abba Kabir Yusuf mu yake bi bashi, saboda ya yi wa Kannywood abubuwan da ba za a taɓa mantawa ba. Misali tun daga muƙamai da ya ba mu a wannan gwamnati tun daga kan Babban Sakatare na Hukumar tace finafinai mataimaka da masu ba shi shawara. Kuma sannan ba a taɓa samun gwamnati da ta mutunta ‘yan Kannywood kamar ta Abba Kabir Yusuf ba. Duba da a shekara ta 2025 gwamna ya bai wa ‘yan Kannywood kujerar aikin Hajji guda shida. Kuma a 2026 nan ma aka ƙara ba mu kujeru, to idan ka duba wannan abu ne na tarihi wanda ba a taɓa samun irin sa ba. Ga makaranta da ta samar ana bai wa ‘yan Kannywood ilimi a ba su tallafin kayan aiki da kuɗaɗe, to ka ga wannan gwamnati mu take bi bashi. Wannan dalili ne ya sa muka bai wa wannan ƙungiya tamu ta Kannywood Awareness Network For Abba Gida’Gida ƙarfin gwiwa domin saka alheri da alheri. Wanda kuma ina tabbatar maka a watan Agusta wannan ƙungiya za ta yi bikin nanu goyon baya ga Maigirma Gwamna Abba Kabir Yusuf kuma mu tabbatar masa da cewa Kannywood tana tare da shi kuma abin da ya yi mana ba mu manta ba, mu ma lokaci ya yi da za mu saka masa da alherin da ya yi mana.

Kuma wannan taron da za mu yi taro ne na masana’antar Kannywood,wanda duk ya yarda yana goyon bayan tafiyar Abba Kabir Yusuf zai zo wannan taron, tun daga babba har yaro za a taru a wannan waje domin nuna cewar mun yarda cewar shi za mu zaɓa a shekara ta 2027, kuma in Allah ya yarda duk wata gudunmawa da ake buƙata za mu bayar  domin ganin mun tabbatar da wannan gwamnati a zaɓe mai zuwa da yardar Allah.

Don haka ina kira ga masu harkar Kannywood su kalli wannan tafiyar tamu ta Kannywood Awareness Network For Abba Gida’Gida kar su kalli cewar tafiya ce da za mu samu kuɗi ko ta wasu mutane. Su kalli cewar gwamnati ta yi mana abin da ya kamata mu biya ta bashin taimakon da ta yi mana, kuma sannan su kalli makomar Jihar Kano, domin zaɓar Abba Kabir Yusuf a 2027 kamar ceton Jihar Kano ne.

Muna fatan za mu samu goyon bayan jama’ar mu  ‘yan Kannywood domin kaiwa ga nasara.

To Madalla mun gode.

Ni ma na gode sosai.

By ukarofi

Leave a Reply