Rikicin FCC: Kwamishinoni sun ja shugabar hukuma zuwa ICPC

Daga jaridar Manhaja

Kwamishinoni masu wakiltar jihohi 36 na kasar nan hada da birnin tarayya Abuja, tare da Hukumar Kyautata Da’ar Ma’aikata ta Kasa (FCC) sun rubuta takardar korafi a kan shugabar hukumar FCC Dr. Muheeba Fraida Dankaka zuwa ga Hukumar Yaki da Rashawa da Laifuka Masu Alaka da Rashawa (ICPC) bisa zarginta da yin ba daidai ba da matsayinta.

Takardar korafin mai dauke da kwanan wata 18/1/2021 wadda ta sami sa hannun Sir Augustine Wokocha da Abdul Wasiu Bawa-Allah, ta nuna yadda shugabar FCC ta mamaye komai na hukumar sannan ta karbe ayyukan kwamishinonin tana mika wa daraktocinta tare da maida wasu ma’aikatan nata ‘yan lelenta.

Kazalika, kwamishinonin sun zargi Muheeba da karkatar da kudaden hukumar ba a bisa ka’ida ba tare da hana kwamishinonin sanin bayanan hada-hadar kudaden ma’aikatar.

Haka nan sun zarige ta da hana su kudaden alawus dinsu na aiki amma ta biya kanta da wasu hadimanta alawus din. Sai kuma batun rashin mutunta kasafin hukumar wanda majalisar kasa ta amince da shi.Da wannan ne, kwamishinonin suka bukaci ICPC ta gudanar da binciken kwakwaf a kan ayyukan FCC tun daga lokacin da aka kafa sabon shugabanci a hukumar a watan Yulin 2020 zuwa yau.

A cewarsu, “Muna so a gudanar da bincike mai zurfi ta hanyar amfani da nagartattun jami’ai wadanda za su yi aiki da gaskiya, sannan a hukunta duk wanda aka samu da hannun cikin badakalar don hakan ya zama darasi ga saura.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *