
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai ba wa Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Daniel Bwala, ya bayyana cewa akwai wasu mutane da ke aiki a matsayin wakilan ‘yan ta’adda acikin rundunonin soji da ‘yan sanda a Nijeriya.
Bwala ya faɗi haka ne yayin wata tattaunawa a shirin The Link Podcast a ranar Juma’a, a lokacin da yake amsa tambaya akan ko Rundunar Sojin Nijeriya na fama da matsalolin wakilan ayyukan ta’addanci.
Ya tunatar da yadda a baya aka riƙa kama jami’an soji da na ‘yan sanda bisa alaƙa da ayyukan ta’addanci a Nijeriya.
Ya ce, “Ba za ka iya cewa babu ba, a ƙashin gaskiya akwai yiwuwar a samu wakili ɗaya ko biyu a soji, ko wani waje daban.”
“An sha kama ‘yan sandanmu da sojojin da ke da hannu a irin wannan al’amari”, inji Bwala.
A cewarsa, hakan abu ne da zai iya faruwa a ko’ina a duniya, yana mai cewa gwamnatin tarayya na ɗaukar matakan da suka dace wajen ganin ta magance matsalolin cigaba da samuwar irin haka acikin jami’an tsaro.
