
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Ingila ta kammala gasar Kofin Duniya na 2026 cikin nasara bayan doke Faransa da ci 6 da 4, inda ɗan wasa Bukayo Saka ya zura ƙwallo uku a wasan.
Wannan ya nuna cewa, Ingila ta samu mafi kyan nasara a gasar acikin shekaru 60.
Wasan, wanda aka buga a filin Miami a yammacin ranar Asabar, ya ɗauki hankalin ‘yan kallo musamman ganin yadda Faransa ta yi ta ƙoƙarin farfaɗowa amma Ingilar ta ƙi ba ta dama, lamarin da ya sa wasan ya zama ɗaya daga cikin irinsa da aka fi zura ƙwallaye masu yawa a tarihin gasar.
Wannan nasara ta zama lallashi ga Ingila bayan shan kaye a wasan kusa da na ƙarshe a hannun Argentina da ci 2 da 1, yayin da ita kuma Faransar ta rasa 2 da 0 a hannun Sifaniya a ɗaya gefen.
A farkon zangon wasan, Ingila ta zura ƙwallo huɗu a ragar Faransa ba tare da ta samu damar farke ko ɗaya ba har aka je hutun rabin lokaci. A yayin haka Saka ya zura biyu.
Bayan koma wa fafatawar ne Faransa ta yi yunƙurin farfaɗowa, inda ta goge biyu ta hannun Kylian Mbappe, sai kuma guda ta Bradley Barcola.
Daga bisani, Saka ya sake jefe ƙwallo a raga a bugun fenareti bayan dukan Djed Spence a kewayen yadi 18 a minti na 86.
Ana zangon ƙarin lokaci ne Osmane Dembele ya sake farke ɗaya, lamarin da ya mayar da wasan 5 da 4. A ƙarshe, Jude Bellingham ya ci ƙwallo mai armashi, wanda hakan ya sa aka kammala wasan 6 da 4.
