Shugaban Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya bayyana cewa hukumar za ta yi nazari kan yiwuwar ƙara yawan ƙasashen da za su halarci Gasar Kofin Duniya daga 48 zuwa 64 kafin gasar shekarar 2030.
Wannan shiri ya biyo bayan nasarar da aka samu a sabon tsarin gasar ta 2026, inda aka ƙara yawan ƙasashen da ke halarta daga 32 zuwa 48, abin da ya bai wa ƙarin ƙasashe 16 damar shiga gasar.
Da yake magana a wata hira, Infantino ya ce za a mika wannan shawara ga kwamitocin da abin ya shafa na FIFA domin su tattauna ta bayan kammala gasar Kofin Duniya ta bana.
“Tabbas wannan batu ne da za a yi nazari a kansa tare da tattauna shi a kwamitocin da abin ya shafa bayan kammala wannan gasa,” inji Infantino.
Ya ƙara da cewa, manufar shirya Kofin Duniya ita ce bai wa dukkan ƙasashen duniya damar mafarkin halartar gasar, ba wai ƙasashen Turai da Kudancin Amurka kaɗai ba.
“Lokacin shirya Kofin Duniya, ya kamata a yi tunanin duniya baki ɗaya. Ya dace kowace ƙasa ta samu damar yin mafarkin shiga wannan gasa.”
Shugaban FIFA ya bayyana cewa faɗaɗa gasar zai bai wa ƙasashe masu tasowa damar nuna ƙwarewarsu, tare da ƙara ingancin wasan ƙwallon ƙafa a duniya.
A cewarsa, ƙwarewar ƙungiyoyi na ci gaba da ƙaruwa a duk nahiyoyi, kuma hana ƙananan ƙasashe shiga gasar na iya rage musu ƙwarin gwiwar ci gaba.
Tun daga Faransa 1998 har zuwa ƙatar 2022, gasar Kofin Duniya na gudana ne da ƙasashe 32.
Sai dai a gasar ta 2026, FIFA ta ƙara adadin zuwa ƙasashe 48, lamarin da ya sa aka buga wasanni 104, mafi yawa a tarihin gasar.
