Kofin Duniya 2026: Manyan ƙasashe huɗu na jadawalin FIFA sun kafa tarihi a wasan kusa da na ƙarshe

Spread the love

Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026 ta kafa sabon tarihi, bayan da karo na farko tun bayan fara gasar maza, ƙasashe huɗu mafi matsayi a jadawalin Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA) suka samu gurbi a wasan kusa da na ƙarshe.

Rahoton BBC Sport ya nuna cewa, bayan buga wasanni sama da 100 tare da cin ƙwallaye fiye da 290 a faɗin Arewacin Amurka, wannan ne karon farko a tarihin gasar da ƙasashe huɗu mafi daraja a jadawalin FIFA suka mamaye matakin wasan kusa da na ƙarshe.

Domin tabbatar da adalci da kuma rage yiwuwar manyan ƙasashe su haɗu tun da wuri, FIFA ta tsara jadawalin gasar ta yadda ƙasashe huɗu mafi matsayi suka kasance a sassa daban-daban na jadawalin wasanni, abin da ya sa ba za su haɗu ba sai a matakin kusa da na ƙarshe.

Bayan kammala wasannin rukuni da kuma fafatawar zagayen fitar da gwani, Faransa, Argentina, Sifaniya da Ingila sun tabbatar da ƙarfinsu tare da kafa manyan wasannin da duniya ke jira.

Faransa ta kai wannan mataki ne bayan doke Moroko da ci 2-0, yayin da Sifaniya ta fitar da Belgium da ci 2-1.

A ɗaya ɓangaren jadawalin kuwa, Ingila ta doke Norway da ci 2-1 bayan ƙarin lokaci, yayin da Argentina ta lallasa Switzerland da ci 3-1 domin samun tikitin zuwa wasan kusa da na ƙarshe.

Hakan ya sa za a ga fafatawa tsakanin ƙasa ta ɗaya a jadawalin FIFA, wato Faransa, da ta uku, Sifaniya, yayin da Argentina mai matsayi na biyu za ta kara da Ingila mai matsayi na huɗu.

Bayan kammala wasannin rukuni da na zagayen fitar da gwani, Faransa (ta 1 a jadawalin FIFA), Argentina (ta 2), Sifaniya (ta 3) da Ingila (ta 4) sun tabbatar da matsayinsu a matsayin manyan ƙasashen awallon ƙafa a duniya, inda suka samu gurbin zuwa wasan kusa da na ƙarshe.

By ukarofi

Leave a Reply