An gano mahaifin tauraron ɗan wasan Faransa Michael Olise tsohon ɗan wasan cricket ne na Nijeriya

Spread the love

An bayyana cewa mahaifin tauraron ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Faransa, Michael Olise, wanda ya haskakawa a Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026, tsohon ɗan wasan ƙungiyar cricket ta ƙasa ta Nijeriya ne.

Rahoton jaridar The Sun Sport ya ce wannan sabon bayani ya jawo hankalin masu sha’awar wasanni, inda ya nuna cewa asalin hazaƙar wasanni a gidan Olise bai taƙaitu ga ƙwallon ƙafa kaɗai ba.

Michael Olise, wanda ke taka leda a ƙungiyar Bayern Munich ta Jamus, na daga cikin fitattun ‘yan wasan da suka taka muhimmiyar rawa a tafiyar tawagar Faransa ƙarƙashin jagorancin kocinta Didier Deschamps a gasar Kofin Duniya ta bana.

Sai dai yayin da yake ci gaba da ɗaukar hankali a filin wasa, wani rahoto ya bayyana tarihin wasanni na iyalinsa, musamman mahaifinsa.

Rahoton ya nuna cewa Vincent Olise, mai shekaru 66 a duniya, ya wakilci ƙungiyar cricket ta ƙasa ta Nijeriya tsakanin shekarun 1983 zuwa 1993.

A matakin cikin gida kuma, ya buga wa ƙungiyar cricket ta Jihar Legas da kuma Foundations Cricket Club, inda ya yi fice saboda bajintarsa.

ɗaya daga cikin manyan nasarorin Vincent Olise ta zo ne a gasar West African ƙuadrangular Tournament, lokacin da Nijeriya ta kara da Gambia.

A wannan wasa, Vincent ya yi abin da ba kasafai ake gani ba a wasan cricket, inda ya fitar da ‘yan wasan hamayya guda goma a zagaye guda (innings ɗaya), lamarin da ya yi daidai da tarihin ƙasar da Chris Enahoro ya kafa a baya.

Michael Olise ya taɓa bayyana cewa mahaifinsa ya taka muhimmiyar rawa wajen gina halayyarsa da ci gabansa tun yana ƙarami.

Ya kuma bayyana cewa duk da kasancewarsa ƙwararren ɗan wasan ƙwallon aafa, wasan cricket na daga cikin wasannin da ya fi sha’awa idan ba ya buga ƙwallo.

By ukarofi

Leave a Reply