Amurka za ta fara karɓar kuɗin amfani da mashigar Hormuz – Trump

Spread the love

Sabuwar sanarwar da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na cewa ƙasarsa za ta fara karɓar kuɗin amfani da mashigar ruwan Hormuz ta sake tayar da muhawara kan ko wata ƙasa na da ikon kakaɓa irin wannan haraji a ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin ruwa na duniya.

Trump ya bayyana cewa idan yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ta rushe, Amurka za ta karɓi kashi 20 cikin ɗari na dukkan kayayyakin da za su ratsa mashigar Hormuz, yana mai cewa hakan zai zama diyya ga rawar da Amurka ke takawa wajen kare tsaron mashigar.

Sanarwar ta zo ne bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta rushe sakamakon saɓanin da ya kunno kai kan ikon da Tehran ke son ci gaba da yi a kan mashigar.

Tun bayan harin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu, Tehran ta rufe mashigar Hormuz, wadda ke zama hanyar da kusan kashi ɗaya cikin biyar na ɗanyen man fetur na duniya da sauran muhimman kayayyaki ke bi. Matakin ya haifar da tashin farashin makamashi tare da girgiza tattalin arzikin duniya.

Duk da cewa furucin na Trump bai samu wani tagomashi a hukumance ba kasancewar a ranar 25 ga Yuni, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana yayin wata ganawa da kasashen Gulf cewa babu wata kasa da ke da ikon karbar kuɗin zirga-zirga a mashigun ruwa na ƙasa da ƙasa.

Rubio ya ce batun karɓar kudin amfani da Hormuz ba zai taɓa kasancewa cikin wata yarjejeniya ba.

Sai dai tun kafin wannan lokaci Trump ya taɓa bayyana cewa idan yarjejeniyar da Iran ba ta tabbata ba, Amurka za ta iya kakaba irin wannan haraji.

A cikin saƙon da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya ce daga yanzu Amurka za ta kasance “Mai kare mashigar Hormuz,” kuma saboda adalci za ta karbi kashi 20 cikin dari na dukkan kayayyakin da ke ratsa mashigar.

Sai dai bai bayyana yadda za a aiwatar da wannan mataki ba, ko kuma wace doka za ta ba Amurka ikon tilasta hakan.

By ukarofi

Leave a Reply