Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC), Hussaini Ishaƙ Magaji (SAN), ya bayyana cewa sabuwar umarnin da hukumar ta fitar kan bayyana wasu muhimman bayanai a takardun kamfanoni ya shafi kamfanonin da aka yi wa rajista ne kawai, bai shafar masu rijistar Sunan Kasuwanci (Business Names) da Amintattun ƙungiyoyi (Incorporated Trustees), ciki har da ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGO).
Magaji ya yi wannan ƙarin haske ne bayan wani lauya, Faisal Manir, ya nemi hukumar ta fayyace matsayin ta sakamakon tambayoyi da dama da jama’a suka riƙa yi kan iyakar sabuwar sanarwar da CAC ta fitar mai taken “Particulars on Company Business Letters” a ranar 7 ga Yuli, 2026.
A martanin da ya mayar, Babban Magatakardar ya bayyana cewa tanade-tanaden da ke cikin sanarwar ba su shafi masu rijistar Sunan Kasuwanci da Amintattun ƙungiyoyi ba, waɗanda suka haɗa da ƙungiyoyin addini, ƙungiyoyin agaji, gidauniyoyi da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu da aka yi wa rajista ƙarƙashin Dokar Kamfanoni da Harkokin Da Suka Shafe Su (CAMA).
Wannan bayani na nufin cewa wajabcin nuna sunan kamfani da lambar rajistarsa a ofisoshi ko wuraren kasuwanci, da kuma saka waɗannan bayanai a takardun kamfani da sauran takardun hukuma, ya taƙaita ne ga kamfanonin da aka yi wa rajista.
Sai dai Magaji ya jaddada cewa, duk da cewa doka ba ta tilasta wa masu Sunan Kasuwanci da Amintattun ƙungiyoyi bin wannan umarni ba, yana da kyau su rungumi irin wannan tsarin domin ƙara inganta gaskiya da riƙon amana a ayyukansu.
“Sanarwar da muka fitar ta shafi kamfanoni ne kawai. Ba ta shafi Sunayen Kasuwanci ko Amintattun ƙungiyoyi ba. Duk da haka, kyakkyawan tsarin shugabanci da gudanarwa na buƙatar su ma su kasance masu gaskiya da bayyana muhimman bayanai,” inji Magaji.
Tun da farko, lauyan Faisal Manir ya rubuta wa CAC yana neman a fayyace ko masu Sunayen Kasuwanci da Amintattun ƙungiyoyi su ma dole ne su riƙa nuna sunan rajistarsu da lambar rajista a wuraren kasuwanci, tare da saka sunayen masu kasuwanci ko amintattun ƙungiyoyi a kan takardun hukuma. Ya bayyana cewa ya nemi wannan ƙarin haske ne saboda yawan tambayoyin da yake samu daga lauyoyi, masu kasuwanci da sauran jama’a kan ko sabuwar dokar ta shafe su.
Ana sa ran wannan bayani zai kwantar da hankalin masu gudanar da kasuwanci da ƙungiyoyi masu zaman kansu da dama, waɗanda suka nuna damuwa kan ko sabon umarnin ya haɗa da su.
Tun farko dai, Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC) ta fitar da sanarwar ne a wani ɓangare na ƙoƙarin ta na ƙarfafa gaskiya da bin ƙa’idojin bayyana bayanai kamar yadda Dokar Kamfanoni da Harkokin Da Suka Shafe Su (CAMA) ta tanada.
Ko da yake sabon bayanin ya taƙaita aiwatar da umarnin ga kamfanoni kaɗai, hukumar ta buƙaci dukkan hukumomi da ƙungiyoyin da aka yi wa rajista su rungumi tsarin gudanarwa mai cike da gaskiya da riƙon amana.
