Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, kuma ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi zargin cewa wasu jami’an gwamnati da bai bayyana sunayensu ba suna shirya masa makirci tare da tsoratar da magoya bayansa yayin da yake gudanar da ziyarar godiya a wasu ƙananan hukumomin jihar.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Pantami ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, bayan ziyarar da ya kai ranar Litinin zuwa ƙananan hukumomin Shongom, Kaltungo da Billiri, inda ya gana da shugabannin jam’iyyarsa da magoya baya.
Ya ce tarbar da aka yi masa ta kasance mai armashi, kuma hakan ya tayar wa wani mutum hankali.
A cewarsa, wannan mutumin ya fara neman bayanan inda zai je domin shirya masa wata muguwar makirci.
“Mu na da ‘yancin yin zirga-zirga a ko’ina cikin Nijeriya kamar yadda Sashe na 41(1) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ya tanada,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa zai kai ziyara zuwa ƙananan hukumomin Akko, Balanga da Yamaltu-Deba, yana mai cewa sun samu labarin wani makirci da ake shiryawa masa a Akko.
Bugu da ƙari, Pantami ya zargi wasu hukumomi da amfani da ƙarfin gwamnati wajen tsoratar da magoya bayansa, har ma da yi musu barazanar kama su saboda goyon bayan da suke ba shi.
Ya ce hakan ya saɓa wa Sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulki, wanda ya bai wa ‘yan ƙasa ‘yancin kafa ƙungiyoyi da shiga cikinsu.
Haka kuma, Pantami ya yi zargin cewa ana ƙoƙarin hana yaɗa bayanai kan wasu kuɗaɗe masu yawa da aka ce an bai wa wasu mawaƙan Hausa daga Kano.
Ya ce ɗaya daga cikin mutanen da ke da alaƙa da lamarin ya fice daga ƙungiyar tare da bayyana gaskiyar abin da ya faru.
Pantami ya buƙaci shugabannin jam’iyyarsa da magoya bayansa su ci gaba da kasancewa masu jajircewa ba tare da tsoron barazana ba.
