Makarantar Tazakiya Islamiyya ta gudanar da bikin yaye ɗalibai karo na biyar a Legas

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

A ranar Lahadin da ta gabata ne Makarantar Tazakiya Islamiyya School da ke yankin Mile 12 International Market a Jihar Legas ta gudanar da bikin yaye ɗalibanta karo na biyar a ƙarƙashin shirinta na takwas.

Makarantar, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Alhaji Muktar Jabo, ɗan asalin Jihar Jigawa, ta yaye ɗalibai maza da mata guda 28, inda maza suka kasance 14, haka kuma mata 14.

Alhaji Muktar Jabo, wanda shi ne shugaban makarantar, ya kuma kasance ɗaya daga cikin fitattun jagororin harkokin kasuwancin busasshen barkono a Legas, tare da riƙe muƙamin shugaban kwamitin kula da harkokin addinin Musulunci a Babban Masallacin Juma’a na ’Yan ɗarika da ke Mile 12.

An gudanar da bikin ne a harabar Mile 12 Primary School, inda taron ya samu halartar shugabannin kasuwar Mile 12, shugabannin makarantun Islamiyya daban-daban, malamai, iyaye da sauran al’ummar Musulmi daga sassa daban-daban na Legas.

Babban Sakataren Kasuwar Mile 12 International Market, Alhaji Balarabe Idris Kibiya, ɗan asalin Jihar Kano, ne ya jagoranci taron tare da wakiltar shugaban kasuwar, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam.

An fara taron ne da addu’o’i da karatun Alƙur’ani Mai Tsarki, inda malamai da magada Annabawa suka yi wa’azi kan muhimmancin bai wa yara ilimin addinin Musulunci da tarbiyya ta gari.

Haka kuma, ɗaliban da aka yaye sun gabatar da karatun Alƙur’ani Mai Tsarki da sauran darussa na addini, abin da ya burge mahalarta taron.

Da yake jawabi a wajen taron, Alhaji Balarabe Idris Kibiya ya isar da saƙon shugaban kasuwar Mile 12, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam, inda ya taya shugabannin makarantar murnar nasarar gudanar da bikin yaye ɗaliban bana.

Ya kuma yi kira ga shugabanni da attajiran kasuwar Mile 12 da su ci gaba da tallafa wa makarantun Islamiyya domin ƙarfafa harkokin ilimin addini a tsakanin yara da matasa.

A nasa jawabin, shugaban makarantar, Alhaji Muktar Jabo, ya gode wa shugabannin kasuwa, malamai, iyaye da sauran baƙi da suka halarci taron tare da bayar da gudunmawa wajen tabbatar da nasarar gudanar da bikin.

Ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka wa duk waɗanda suka taimaka da alheri, Ya kuma mayar da baki gidajensu lafiya.

Alhaji Muktar ya kuma jaddada ƙudirin makarantar na ci gaba da koyar da ilimin Alƙur’ani da tarbiyyar Musulunci domin samar da al’umma ta gari mai anfani ga addini da ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply