Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE
Jami’ar hulɗa ta UN Women a Jihar Yobe, Ambasada Fatima Mohammed Paga, ta yaba wa gwamnatin Jihar Yobe bisa tallafa wa mata masu sana’ar ƙosai da murhunan girki masu amfani da makamashi mai tsafta, tare da ba su wake da man girki.
Tana mai bayyana shirin a matsayin wani gagarumin mataki na ƙarfafa tattalin arzikin mata da kare muhalli.
Shirin, wanda ma’aikatar ƙirƙirar arziki da ƙarfafa tattalin Alarziki ta Jihar Yobe ta aiwatar, ya bai wa mata masu cin gajiyar murhunan girki da makamashi, buhunan wake da man girki domin bunƙasa sana’o’insu da ƙara musu kuɗaɗen shiga.
A cikin wata sanarwa da Fatima Paga ta sanyawa hannu tare da raba wa manema labarai, Ambasada Paga ta yaba wa Gwamna Mai Mala Buni bisa ƙaddamar da shirin, tana mai cewa ya nuna ƙudirin gwamnati na tallafa wa mata, waɗanda su ne suka fi rinjaye a sana’ar sayar da ƙosai a faɗin jihar.
Ta ce tallafin zai rage kuɗin da mata ke kashewa wajen gudanar da sana’arsu, ya ƙara musu riba, tare da ƙarfafa amfani da murhunan girki marar hayaki
A cewarta, hakan zai rage dogaro da itace da sauran makamashin da ke gurɓata muhalli, tare da taimakawa wajen yaƙi da sauyin yanayi da inganta lafiyar al’umma.
Ambasada Paga ta kuma bayyana cewa ƙarfafa tattalin arzikin mata na taimakawa wajen inganta rayuwar iyalai, samar da hanyoyin samun abin dogaro mai ɗorewa, da kuma cimma manufofin cigaba mai ɗorewa (SDGs), musamman waɗanda suka shafi daidaiton jinsi, rage talauci da kare muhalli.
Ta ce, “Wannan shiri ya nuna ƙudirin Gwamnatin Jihar Yobe na inganta walwalar mata tare da magance matsalolin muhalli ta hanyar amfani da sabbin hanyoyin makamashi masu ɗorewa.”
A ƙarshe, ta buƙaci gwamnatin jihar da ta ci gaba da aiwatar da irin waɗannan shirye-shiryen da ke bunƙasa sana’o’in mata da amfani da makamashi mai tsafta, tana mai jaddada cewa UN Women za ta ci gaba da mara wa irin waɗannan tsare-tsare baya domin faɗaɗa damar tattalin arziki ga mata da kuma bunƙasa ci gaba mai ɗorewa a Jihar Yobe.
