Daga DAUDA USMAN a Legas
Mataimakin Shugaban Kasuwar ’Yan Gwari da ke garin Ogere a Jihar Ogun, Alhaji Muhammed Sani S. Kure, ya bayyana cewa kasuwar na ci gaba da samun gagarumin ci gaba a harkokin kasuwanci da zaman lafiya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasuwar, Alhaji Mahammadu Bura Gwani.
Alhaji Muhammed Sani ya bayyana hakan ne a ofishin kasuwar da ke Ogere yayin da yake zantawa da wakilan kafafen yaɗa labarai kan yadda harkokin kasuwancin Gwari ke gudana a jihar.
Ya ce, a halin yanzu kasuwar tana samun ci gaba ta fannoni daban-daban, musamman wajen bunƙasa kasuwanci, tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai tsakanin ‘yan kasuwa da kuma inganta hulɗa tsakanin mambobin kasuwar.
Ya yaba wa shugaban kasuwar, Alhaji Mahammadu Bura Gwani, bisa irin shugabanci nagari da yake yi wajen haɗa kan al’ummar kasuwar da kuma kawo sauye-sauye masu amfani ga harkokin kasuwanci.
Alhaji Muhammed Sani ya kuma yi kira ga shugabanni da manyan ‘yan kasuwar Gwari da ke Ogere da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da haɗin kai tsakaninsu da sauran ƙabilun da ke zaune a Jihar Ogun.
Haka kuma ya buƙaci ‘yan kasuwar da su ci gaba da bai wa shugabannin kasuwar cikakken goyon baya domin su samu damar aiwatar da shirye-shiryen da za su ƙara bunƙasa kasuwar.
Da yake magana kan halin tattalin arziki, Mataimakin shugaban kasuwar ya nuna damuwarsa kan hauhawar farashin man fetur da tasirin da yake yi ga harkokin kasuwanci da rayuwar al’umma.
Ya ce, wannan yanayi na iya jefa harkokin kasuwanci cikin koma baya, saboda haka ya yi kira ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta ƙara ɗaukar matakan da za su rage wa ‘yan ƙasa raɗaɗin tsadar rayuwa.
Har ila yau, ya shawarci matasan Arewacin Nijeriya da su rungumi neman ilimi da koyon sana’o’in hannu domin su dogara da kansu, su guji zaman kashe wando tare da samun ingantacciyar rayuwa.
A ƙarshe, Alhaji Muhammed Sani S. Kure ya yabawa Sarkin Hausawan Ogere, Alhaji Abdullahi Abubakar, bisa irin ƙoƙarin da yake yi wajen kare muradun Hausawan da ke zaune a garin da kuma inganta zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’ummomi.
Sannan ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Nijeriya baki ɗaya.
