Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen ƙaramar hukumar Argungu a Jihar Kebbi, Alhaji Hara Akote Badariya, ya ce ɗaukar doka a hannu ne babban abin da ke haddasa rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a yankin.
Alhaji Akote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da wakilin Blueprint Manhaja a garin Argungu.
Ya ce, tun shekaru aru-aru manoma da makiyaya sun kasance suna rayuwa tare cikin fahimtar juna, yana mai cewa kowanne ɓangare na da buƙatar ɗayan wajen ci gaban rayuwa.
A cewarsa, idan makiyaya sun yi ɓarna a gonaki, al’ada ta kasance a sasanta lamarin cikin lumana, ko kuma a kai ƙara gaban hukumomi idan abin ya fi ƙarfin sasantawa.
“Abin da bai dace ba shi ne rikici ya rikiɗe zuwa faɗa da kashe-kashe. Wannan ba al’adar kakanninmu ba ce,” inji shi.
Ya bayyana cewa, saboda tsoron hare-hare, makiyaya da dama sun fara tura ƙananan yara wajen kiwo, domin idan suka samu matsala suna iya tserewa, saɓanin manya da kan tsaya su fuskanci rikici.
A cewarsa, irin wannan yanayi ne ya taimaka wajen haddasa rikicin da ya faru a garin Gulma a kwanakin baya, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane takwas.
Alhaji Akote ya yi kira ga Fulani makiyaya da su guji ɗaukar fansa idan aka yi musu wani abu, yana mai ba su shawarar su bar komai a hannun Allah tare da bai wa hukumomin tsaro damar gudanar da bincike da hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin kashe-kashen.
Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu dangantaka tsakanin Fulani da mazauna yankin ta inganta sosai, inda ya ce yanzu Fulani na shiga cikin gari suna hulɗa da jama’a har zuwa tsakar dare, sabanin shekarun baya da suke barin gari tun da yamma saboda rashin tsaro.
A ƙarshe, shugaban na Miyetti Allah ya yi kira ga manoma da su guji ɗaukar doka a hannunsu idan suka samu matsala da makiyaya. Ya buƙace su da su riƙa kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa domin a bi hanyar doka wajen warware duk wata takaddama.
