Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta gudanar da taron jin ra’ayoyin jama’a kan kasafin kuɗin 2027 a mazaɓu 361 da ke faɗin jihar.
A jawabin bude taron na mazaɓar sa da ke Raɗɗa a ƙaramar hukumar Charanchi, Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana son jama’a su bada gudunmuwa yasa gwamnatin sa ta shirya wannan taron da zai taimakawa gwamnati wajan tsara kasafin kuɗi na 2027.
Ya ce lokaci ya wuce da gwamnati za ta zaune ta tsara kasafin kuɗi ba tare da gudummawar al’umma ba.
Gwamnan sai ya jawo hankalin al’ummar jihar da kada su ɗauka duk buƙatar da suka gabatar na mazaɓar su gwamnati za ta aiwatar.
Dole mu zauna mu tantance muhimman abubbuwan da za su aiwatar da zai daidai da kasafin kuɗin jihar.
Darakta janaral na hukumar bunƙasa kasuwanci ta jihar (KASEDA), Dr. Babangida Kabir Rumah a nasa jawabi, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa wajen bunƙasa ƙanana, matsakaita da ƙananan masana’antu a jihar.
Dr. Babangida Kabir Rumah ya bayyana cewa taron wata dama ce ta tattara shawarwari da ra’ayoyin masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa ci gaban harkokin kasuwanci da bunƙasa tattalin arzikin Jihar Katsina.
To sai da al’ummar ƙauyukan Ika,Kadandani zuwa Remawa a ƙaramar hukumar Rimi sun ɗaga hannun suna nuna wa gwamna Raɗɗa cewa su hanya suke buƙata gwamnati ta gina masu.
Gwamnan a wani taro daban ya sanar da cewa gwamnati za tayi wani abu a kai.
