Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da ƙoƙarin rusa jam’iyyun adawa ta hanyar haddasa rikice-rikice a cikinsu.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a ranar Litinin, Atiku ya ce matakin da INEC ta ɗauka kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC na nuna son kai, kuma zai iya jawo sabon rikici a jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
Zargin Atiku ya biyo bayan ikirarin Nafiu Bala Gombe cewa ya loda sunayen ‘yan takarar ADC a shafin INEC, bayan samun lambar shiga tsarin daga hukumar.
Sai dai Atiku ya ce Sanata Daɓid Mark ne shugaban ADC da INEC ta amince da shi, don haka bai kamata a bai wa wani daban damar gabatar da sunayen ‘yan takara ba.
Ya ce matakin bai wa Nafiu Bala Gombe damar shiga tsarin INEC ya saɓa wa doka da ƙa’idojin hukumar, yana mai jaddada cewa jam’iyya ba za ta iya samun shugabanni biyu da INEC ta amince da su ba.
Atiku ya kuma ce bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe, ‘yan takara dole ne su fito ta hanyar sahihin zaɓen fidda gwani, kuma duk wata takara da ba ta bi wannan tsari ba, ba ta da inganci.
Ya buƙaci INEC ta guji ɗaukar matakan da za su haddasa rikici a cikin jam’iyyun adawa, yana mai zargin shugaban hukumar da taimakawa wajen raunana adawa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, INEC ba ta mayar da martani kan zarge-zargen ba.
