Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf bai taɓa miƙa masa ragamar tafiyar da harkokin jihar ba a duk lokacin da yake fita tafiye-tafiye na aiki.
Gwarzo ya bayyana hakan ne yayin da yake waiwaye kan yadda alaƙarsa da gwamnan ta kasance kafin saɓanin siyasa ya raba su.
A cewarsa, duk lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf zai yi tafiya, ko ta cikin gida ko ta ƙasashen waje, abin da kawai yake yi shi ne sanar da shi cewa zai yi tafiya, ba tare da ba shi umarnin kula da harkokin gwamnatin jihar ba.
“Ko sau ɗaya bai taɓa ce min ‘ka riƙe Kano’ ba. Ko zai je Nijar, Saudiyya ko Ingila, sai dai ya kira ya sanar da ni cewa zai yi tafiya. Bai taɓa nuna kamar yana damƙa min ragamar mulkin jihar ba,” inji Gwarzo.
Kalaman tsohon mataimakin gwamnan sun sake tayar da muhawara kan irin alaƙar da ta kasance tsakaninsa da Gwamna Yusuf kafin rikicin siyasa ya raba su.
Gwarzo ya bar gwamnatin Kano kafin daga bisani ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC domin tunkarar zaɓen shekarar 2027.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin Jihar Kano ko kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ba su fitar da wata sanarwa da ke mayar da martani kan ikirarin da Gwarzo ya yi ba.
