Mutumin da ya bari macizai 200 suka sare shi ya taimaka wa masana samar da rigakafi

Spread the love

Wani Ba’amurke mai suna Tim Friede ya ja hankalin masana kimiyya bayan sun gano cewa jininsa na iya zama mabuɗin samar da sabon maganin dafin maciji da zai iya ceton rayukan dubban mutane a faɗin duniya.

Rahotanni sun nuna cewa Friede ya shafe kusan shekaru 20 yana bari nau’o’in macizai masu dafi su cije shi da gangan, inda aka ce ya sha cizo fiye da sau 200, sannan ya yi amfani da allurar dafin maciji fiye da sau 650 domin jikinsa ya saba da dafin.

Masana daga wani kamfanin binciken kimiyya da ke Amurka sun ce gwaje-gwajen da suka gudanar sun nuna cewa ƙwayoyin rigakafin da ke cikin jininsa na iya taimakawa wajen ƙirƙirar maganin da zai yi tasiri kan nau’o’in macizai masu dafi da dama, maimakon irin magungunan da ake da su yanzu waɗanda galibi ke aiki ne kan nau’i ɗaya ko kaɗan.

Masana sun bayyana wannan a matsayin babban ci gaba a fannin lafiya, musamman idan aka yi la’akari da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce dubban mutane na mutuwa a kowace shekara sakamakon cizon macizai.

By ukarofi

Leave a Reply