Wani mai kula da namun daji ya rasa ransa bayan wasu zakuna sun kai masa hari a wani gidan zoo da ke jihar ƙueensland a ƙasar Australia.
Rahotanni sun bayyana cewa mamacin, wanda ya shafe shekaru yana aiki da zakuna da sauran namun daji, ya shiga wurin da ake killace zakunan ne domin gudanar da aikinsa na yau da kullum. Sai dai, cikin ɗan lokaci, ɗaya ko fiye da ɗaya daga cikin zakunan suka afka masa.
An yi gaggawar kai ɗauki, amma duk da aoƙarin ceto rayuwarsa, ya rasu sakamakon munanan raunukan da ya samu.
Mahukuntan gidan namun dajin sun ce an fara gudanar da bincike domin gano yadda lamarin ya faru, tare da duba ko an samu wata matsala ta tsaro ko kuskure yayin gudanar da aikin. Sun kuma tabbatar da cewa ba a kashe zakunan ba, domin harin na ci gaba da zama abin bincike.
Lamarin ya sake tayar da hankali kan haɗarin da masu kula da manyan dabbobi ke fuskanta duk da gogewa da ƙwarewar da suke da ita.
