Matatar Dangote ta koma karɓar Dala wajen cinikayya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sake tsanantar rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ya sake jefa kasuwar ɗanyen mai ta duniya cikin ruɗani, yayin da farashin mai ya yi tashin gwauron zabo sakamakon fargabar katsewar samar da mai, yiwuwar ƙarin takunkumi da kuma barazanar tsaro a mashigar ruwan Hormuz, wadda ke daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai a duniya.

A daidai wannan lokaci ne kuma Matatar Mai ta Dangote ta sanar da sauya tsarin sayar da kayayyakinta, inda ta dakatar da karɓar kuɗin naira tare da fara sanya farashin man fetur (PMS), dizal da man jiragen sama (ATK) da dalar Amurka.

Rahotanni sun bayyana cewa matatar ta ƙayyade farashin man fetur daga matatar zuwa dala 0.779 kan kowace lita, lamarin da ya kawo ƙarshen tsarin biyan kuɗi da naira da aka fara amfani da shi bayan ƙaddamar da shirin musayar ɗanyen mai da naira na Gwamnatin Tarayya a ranar 1 ga Oktoban 2024.

Masana sun bayyana cewa wannan mataki na Matatar Dangote zai iya sauya tsarin farashin man fetur a ɓangaren kasuwancin mai da aka cire tallafi (downstream sector), kasancewar matatar ta zama babbar mai samar da tataccen mai a Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply