Rangwamen harajin shigo da kaya ya kai tiriliyan N34 – Kwastom

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Kwastom ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa darajar takardun amincewa da rangwamen harajin shigo da kaya (IDEC) da aka bayar a shekarar 2025 ta kai kusan Naira tiriliyan 34, lamarin da ya yi tasiri sosai ga kuɗaɗen shiga na hukumar.

Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya gurfana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kuɗi a zaman sauraron bincike da aka gudanar da hukumomin gwamnati masu tara kuɗaɗen shiga a Abuja.

Ya ce duk da cewa Hukumar Kwastom ta Nijeriya na cikin manyan hukumomin da ke samar wa gwamnati kuɗaɗen shiga, manufofin gwamnati kan harkokin kuɗi, musamman na ba da rangwamen harajin shigo da kaya, na rage yawan kuɗin da hukumar ke tarawa.

A cewarsa, tsarin IDEC da aka fara aiwatarwa tun watan Maris na shekarar 2020 na daga cikin manyan abubuwan da ke tasiri ga kuɗaɗen shigar hukumar.

Ya ce kusan kashi 60 cikin 100 na rangwamen harajin da aka bayar a shekarar 2025 ya shafi shigo da kayan aikin soja, waɗanda aka ware daga biyan haraji saboda matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Adeniyi ya ƙara da cewa sauran rangwamen sun haɗa da shigo da kayan amfani da iskar gas ta CNG, motocin lantarki da na haɗaɗɗen makamashi, kayan aikin asibiti da magunguna, injinan masana’antu da kayan samarwa, da kuma kayan abinci da gwamnati ta amince a shigo da su domin rage matsin tattalin arziki.

Ya jaddada cewa bai kamata a duba manufofin haraji ta fuskar tara kuɗi kaɗai ba, domin da yawa daga cikin rangwamen an samar da su ne domin bunƙasa masana’antu, inganta harkokin lafiya da cimma wasu manyan manufofin tattalin arziki.

Sai dai ya ba da shawarar a ƙara ƙarfafa tsarin sa ido domin tabbatar da cewa waɗanda suka amfana da rangwamen sun cimma manufar da aka ba su, ciki har da rage farashin kaya, ƙara yawan samar da kayayyaki a masana’antu da kuma sauƙaƙa samun ingantattun ayyukan lafiya.

Shugaban Hukumar Kwastom ya kuma bayyana cewa zuwa ranar 30 ga Yunin 2026, hukumar ta tara Naira tiriliyan 4.5 daga cikin burinta na tara Naira tiriliyan 11.04 a wannan shekara, lamarin da ke nuna cewa har yanzu akwai kusan Naira tiriliyan 7 da ake sa ran za a tara kafin ƙarshen shekarar kasafin kuɗi.

A wani ɓangare kuma, Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kuɗi ya yi barazanar ɗaukar mataki kan wasu hukumomin gwamnati da suka ƙi amsa gayyatar da aka yi musu domin halartar zaman binciken.

Hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA), Hukumar Bunƙasa ƙanana da Matsakaitan Masana’antu ta Nijeriya (SMEDAN), Asusun Horar da Ma’aikata na Masana’antu (ITF) da kuma Asibitin Kiwon Lafiya na Tarayya da ke Jabi (FMC Jabi).

Har ila yau, kwamitin ya saurari zargin da Hukumar Kula da Bin Dokokin Kasafin Kuɗi (FRC) ta yi cewa Hukumar Kwastom tana bin gwamnati bashin Naira biliyan 8.9 na rarar kuɗaɗen gudanar da aiki da ya kamata ta tura cikin Asusun Haɗaɗɗen Kuɗaɗen Shiga na Tarayya, tun daga shekarar 2019. Sai dai Hukumar Kwastom ta musanta zargin.

Bugu da ƙari, kwamitin ya duba zargin cewa Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Nijeriya (CAC) ba ta mayar wa gwamnati Naira biliyan 13.9 na rarar kuɗaɗen gudanar da aiki tsakanin shekarun 2023 zuwa 2025 ba.

Da yake mayar da martani, Babban Magatakardar Hukumar CAC, Hussaini Ishaƙ Magaji, ya ce hukumar na ci gaba da biyan kuɗaɗen da ake bin ta a matakai.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kuɗi, Sanata Sani Musa (Neja ta Gasar), ya umarci Hukumar CAC da Hukumar Kula da Bin Dokokin Kasafin Kuɗi tare da sakatariyar kwamitin da su daidaita bayanansu sannan su gabatar da cikakken rahoto cikin makonni biyu. Ya kuma yi gargaɗin cewa shugabannin hukumomin da suka ƙi halartar zaman, ciki har da NCAA, ITF, SMEDAN da FMC Jabi, dole ne su halarci zama na gaba ko kuma su fuskanci hukuncin da dokokin Majalisar Dattawa suka tanada.

By ukarofi

Leave a Reply