Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ɗarikar ƙadiriyya, Sheikh ƙaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya kai ziyara ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a Abuja, a wani mataki da masu sa ido kan harkokin siyasar Kano ke ganin na ƙara nuna yadda goyon bayan manyan malamai ke ƙaruwa ga gwamnan.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan irin goyon bayan da wasu manyan ƙungiyoyin addinin Musulunci da malamai ke bai wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf da kuma yiwuwar tasirin hakan a siyasar jihar nan gaba.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Talata, ya bayyana cewa wannan ita ce ganawa ta farko tsakanin Gwamna Abba da Sheikh ƙaribullah tun bayan kafa gwamnatin jihar.
A yayin ziyarar, Sheikh ƙaribullah ya taya gwamnan murnar nasarorin da gwamnatinsa ta samu, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ƙara masa hikima, lafiya da nasara wajen gudanar da mulki.
Malamin ya yaba da ayyukan ci gaban da gwamnatin jihar ke aiwatarwa, musamman a fannonin gine-ginen more rayuwa, ilimi, lafiya da sauran muhimman sassa, yana mai ƙarfafa gwamnan da ya ci gaba da aiwatar da manufofin da za su amfani al’umma.
Hakazalika, shugaban ɗarikar ƙadiriyya ya tabbatar wa gwamnan da ci gaba da addu’o’i da goyon bayan mabiya darikar domin samar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.
Da yake nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa Sheikh ƙaribullah bisa ziyarar, yana mai bayyana ta a matsayin wata alama ta kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin gwamnati da shugabannin addini.
Ya kuma buƙaci malamai da mabiya ƙungiyoyin addinin Musulunci su ci gaba da yi wa ƙasa addu’o’in zaman lafiya, bunƙasar tattalin arziki da haɗin kai, yana mai jaddada cewa addu’o’in malamai na taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar kowace gwamnati.
Gwamnan ya sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi jin daɗin al’umma da kuma bunƙasa ci gaba a faɗin Jihar Kano.
