Ta nemi saki bayan ChatGPT ya sa ta zargi mijinta da cin amana

Spread the love

Wata mata a ƙasar Girka ta tayar da ƙura bayan ta shigar da ƙarar neman saki daga mijinta, tana mai cewa amsoshin da ta samu daga manhajar AI ta ChatGPT ne suka sa ta fara zargin cewa mijin nata yana cin amanarta.

Rahotanni sun ce matar ta yi amfani da ChatGPT ne wajen neman fassarar wasu abubuwa da suka shafi rayuwarta da mijinta, ciki har da hoton ragowar kofi da ta sha. Ana zargin manhajar ta ba da amsar da ta sa matar ta yi imanin cewa mijinta na hulɗa da wata mata.

An ce bayan samun wannan amsa, matar ta fara taƙaddama da mijinta kafin daga bisani ta nemi a raba aurensu.

Lamarin ya bazu sosai a kafafen sada zumunta, inda ya haifar da muhawara tsakanin masu amfani da fasahar basirar wucin gadi. Yayin da wasu suka ce bai kamata mutane su dogara da AI wajen yanke manyan hukuncin rayuwa ba, wasu kuma sun jaddada cewa dole ne a tabbatar da duk wani zargi ta hanyar hujjoji na zahiri, ba wai amsar wata manhaja kaɗai ba.

Masana fasaha kuma sun yi gargaɗin cewa ChatGPT da makamantansa ba kayan tantance gaskiya ba ne, kuma bai kamata a yi amfani da su wajen yanke hukuncin da zai shafi rayuwar aure ko wasu muhimman al’amura ba.

By ukarofi

Leave a Reply