Fitattun taurarin Najeriya da suka rungumi Musulunci: Yadda sauyin addini ya jawo ce-ce-ku-ce da jan hankali

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

A Najeriya, addini ba kawai wata alaƙa ce tsakanin mutum da Ubangijinsa ba. Wani ɓangare ne da ke da tasiri a rayuwar al’umma, zamantakewa da al’adu. Saboda haka, duk lokacin da fitaccen mutum ya sanar da sauya addininsa, lamarin kan ɗauki hankalin jama’a, ya haifar da ce-ce-ku-ce tare da jan ra’ayoyi mabambanta.

A shekarun baya-bayan nan, an samu wasu fitattun ‘yan wasan Nollywood, mawaƙa da masu ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a kafafen sada zumunta da suka bayyana cewa, sun rungumi addinin Musulunci bayan sun taso a gidajen Kirista ko kuma bayan sun daɗe suna bin addinin Kirista. Wasu sun bayyana dalilan da suka sa suka ɗauki wannan mataki, yayin da wasu kuma suka zaɓi su ci gaba da rayuwarsu ba tare da yawan magana a kan batun ba.

Abin lura shi ne, mafi yawan waɗanda suka yi irin wannan sauyi sun jaddada cewa matakin da suka ɗauka ya samo asali ne daga bincike, fahimta ko kuma zaɓin kansu, ba wai tilastawa ba.

Shafin Taurari na wannan makon zai kawo maku jerin waɗannan taurarin tun daga jaruman fim zuwa mawaƙa tare kuma da fitattun ‘yan soshiyal midiya da suka zaɓi addinin Musulunci bayan sun kasance mabiya na Kiristoci tsayin lokaci. 

Bukky Wright:

ɗaya daga cikin fitattun jaruman da aka fi dangantawa da wannan sauyi ita ce tsohuwar jarumar Nollywood, Bukky Wright. An haife ta ne a gidan da ya haɗa addinai biyu, inda mahaifinta Kirista ne, mahaifiyarta kuma Musulma ce. Duk da wannan yanayi, daga baya ta bayyana kanta a matsayin Musulma, lamarin da ta sake tabbatarwa a shekarar 2024 lokacin da ta taya al’ummar Musulmi murnar watan Ramadan tare da bayyana godiyarta ga Allah. Haka kuma, an ga jarumar tana gudanar da ibadu a ƙasar Saudiyya, abin da ya ƙara tabbatar da yadda ta rungumi sabon salon rayuwarta.

Burna Boy:

A ɓangaren waƙa kuwa, mawakin Afrobeats da ya lashe kyautar Grammy, Burna Boy, ya jawo hankalin duniya a ƙarshen shekarar 2025 bayan ya bayyana a wani shirin tattaunawa cewa ya rungumi Musulunci. Mawaƙin ya ce bai ɗauki wannan mataki cikin gaggawa ba, sai bayan shekaru na nazari da neman fahimtar al’amuran addini. Kalamansa sun bazu a kafafen sada zumunta, inda suka haifar da martani iri-iri daga masoya da masu bibiyar harkokin nishaɗi.

L.A.ɗ:

Shi ma fitaccen mawaƙi L.A.ɗ, wanda ya yi fice da waƙar ‘Caro’, ya bayyana a matsayin Musulmi duk da cewa wasu daga cikin iyalansa Kiristoci ne. A wani lokaci, ya bayyana farin cikinsa bayan ya samu damar bikin ranar haihuwarsa a birnin Makkah, yana mai cewa wannan buri ne da ya daɗe yana fata ya cika.

Priscilla Ojo:

ɗaya daga cikin labaran da suka fi ɗaukar hankali a ‘yan kwanakin nan shi ne na Priscilla Ojo, ‘yar fitacciyar jaruma Iyabo Ojo. Rahotanni sun nuna cewa ta rungumi Musulunci bayan aurenta da mawaƙin Tanzaniya Juma Juɗ. Shi kansa Juma Juɗ ya bayyana cewa bai yi amfani da matsin lamba wajen neman matarsa ta karɓi Musulunci ba, illa ya bi hanyar tattaunawa da ilmantarwa kamar yadda malamai suka ba shi shawara. Daga baya ne aka ce ta amince da addinin, tare da ɗaukar sunan Hadizah.

Mercy Aigbe:

A shekarar 2023 kuma, fitacciyar jarumar Nollywood Mercy Aigbe ta sanar da rungumar Musulunci bayan aurenta da mai shirya fina-finai Kazim Adeoti. Bayan wannan sauyi, ta fara amfani da sunan Hajia Meenah, kuma tun daga lokacin ake yawan ganinta tana halartar wasu ibadu da bukukuwan Musulunci tare da mijinta.

Mo Bimpe:

Ita ma Mo Bimpe, wato Adebimpe Oyebade, ta karbi Musulunci bayan aurenta da fitaccen jarumi Lateef Adedimeji a shekarar 2021. Bayan sauyin addininta, ta fara amfani da sunan Rahmah ko Rahmatullah, lamarin da ya jawo taya ta murna daga wasu da kuma ce-ce-ku-ce daga wasu mabiyanta.

Lizzy Anjorin:

A cikin jerin akwai kuma Lizzy Anjorin, wadda ta bayyana cewa ta taso ne a gida mai haɗe da addinai biyu kafin daga baya ta zaɓi rungumar Musulunci. Tun bayan sauyin nata, ta gudanar da aikin Hajji kuma ta ci gaba da bayyana kanta a matsayin Musulma duk da ci gaba da amfani da sunan Lizzy Anjorin a harkar fim.

Debbie Shokoya:

Jaruma kuma mai shirya fina-finai Debbie Shokoya ta ce sauyin addininta bai samo asali daga tilastawa ba. A cewarta, zaɓin da ta yi ya ginu ne a kan abin da ta yi imani da shi bayan aure, tare da bayyana cewa ta rungumi Musulunci ne saboda fahimta da kusancinta da Allah. Bayan haka ta ɗauki sunan Mutmaina.

Chef T:

Shahararriyar mai koyar da girki kuma mai wallafa girke-girke a intanet, Chef T (Diary of a Kitchen Lover), ta bayyana a shekarar 2026 cewa ta karɓi Musulunci tun kusan shekara goma da suka gabata, amma ta zaɓi ɓoye wannan batu har sai da ta ga lokacin da ya dace ta sanar da mabiyanta. Ta jaddada cewa babu wanda ya tilasta mata yin hakan.

Kizz Daniel:

Game da Kizz Daniel, rahotanni sun nuna cewa ya ƙara bayyana alaƙar da yake da Musulunci a ƙarshen shekarar 2025. Mawaƙin, wanda aka haifa cikin iyali mai haɗe da addinai, ya taba bayyana cewa sunansa na Musulunci Dhikrullah ne. Sai dai wasu daga cikin bayanan da suka shafi sauyin addininsa sun ci gaba da kasancewa abin ce-ce-ku-ce, saboda haka ba dukkansu ne aka tabbatar da su daga ɓangarensa kai tsaye ba.

Masana harkokin zamantakewa sun ce irin waɗannan sauye-sauyen addini kan jawo hankalin jama’a ne saboda shaharar mutanen da abin ya shafa, ba wai don addinin kansa ba. Sun kuma yi nuni da cewa a cikin al’umma mai cike da bambancin addinai irin Najeriya, irin wannan batu na iya tayar da muhawara, amma a karshe addini lamari ne da ya shafi mutum da abin da ya yi imani da shi.

Duk da bambancin ra’ayoyi da ake samu bayan sanar da irin waɗannan sauye-sauye, abin da ya fi fito wa fili shi ne cewa yawancin waɗanda abin ya shafa sun dage cewa sun ɗauki matakin ne bayan nazari da fahimta, kuma suna fatan a mutunta zaɓinsu kamar yadda su ma suke mutunta aƙidar sauran mutane.

Hakan ya sake nuna cewa rayuwar shahararru ba ta taƙaitu ga fina-finai ko waƙoƙi kadai ba. Duk wani muhimmin mataki da suka ɗauka, musamman wanda ya shafi addini ko zamantakewa, kan zama abin da al’umma ke bibiya, suna tattaunawa a kai, kuma wani lokaci yana zama darasi kan yadda ake kallon ‘yancin mutum na zaɓar aƙidarsa.

By ukarofi

Leave a Reply