Tehran na amfani da Houthis wajen barazanar rufe Bab el-Mandeb domin matsa wa Amurka lamba

Spread the love

Bayan da rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka ya jefa mashigar ruwan Hormuz cikin mawuyacin hali, alamu na nuna cewa Tehran na karkata hankalinta zuwa wata muhimmiyar mashigar ruwa ta duniya, Bab el-Mandeb, wadda ke hada Bahar Maliya da Tekun Aden, domin ƙara matsa wa Washington lamba tare da jefa harkokin makamashi da kasuwancin duniya cikin sabon yanayi na rashin tabbas.

Rahotanni da masana suka tattauna da kamfanin dillancin labarai na Reuters sun bayyana cewa yayin da hare-haren Amurka ke ƙara zurfafawa cikin Iran, sannan mayakan Houthis masu samun goyon bayan Tehran ke ƙara kai hare-hare daga Yemen, gwamnatin Iran na ƙoƙarin faɗaɗa filin rikicin daga fagen soja zuwa tattalin arzikin duniya.

A cewar masana, bayan Iran ta nuna irin tasirin da za ta iya yi a mashigar Hormuz, yanzu tana nuna alamun cewa za ta iya amfani da kawarta ta Houthis wajen kawo cikas a mashigar Bab el-Mandeb, wata muhimmiyar hanya da jiragen dakon mai da sauran kayayyaki daga ƙasashen Gabas ta Tsakiya ke bi zuwa Turai da sauran sassan duniya.

A ranar Litinin, wani babban jami’in ƙasar Yemen ya bayyana cewa dakarun ƙasar a shirye suke su rufe mashigar Bab el-Mandeb idan Saudiyya ta ci gaba da kai hare-hare a Yemen. Kalaman nasa, kamar yadda gidan talabijin na Press TV na Iran ya ruwaito, sun nuna cewa irin wannan mataki na iya haddasa tashin farashin danyen mai har ya kai dala 200 kan ganga guda.

Mohammed al-Farah, mamba a ofishin siyasar ƙungiyar Ansarullah wadda aka fi sani da Houthis, ya zargi Amurka da karfafa wa Saudiyya gwiwa wajen kai hare-hare kan Yemen.

Ya ce idan rikicin ya kara ƙamari, za a iya rufe mashigun Hormuz da Bab el-Mandeb a lokaci guda, lamarin da zai haifar da mummunan tashin farashin mai da kuma girgiza tattalin arzikin duniya.

Masana harkokin Gabas ta Tsakiya sun bayyana cewa idan Hormuz ita ce babbar katin dabarun Iran, to Bab el-Mandeb ita ce wata babbar dama ta biyu da Tehran za ta iya amfani da ita idan rikicin ya ƙara tsananta.

Farfesa Fawaz Gerges, kwararre kan harkokin Gabas ta Tsakiya, ya shaida wa Reuters cewa Iran na son nuna wa Amurka cewa tana da ikon jefa manyan mashigun ruwa guda biyu cikin hadari lokaci guda.

A cewarsa, sakon Tehran shi ne cewa ba Hormuz kadai ba, har ma da Bab el-Mandeb na iya zama wurin da rikicin zai rikide zuwa babbar barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa da kasuwancin makamashi na duniya.

By ukarofi

Leave a Reply