Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauki wani sabon mataki na aiwatar da shirin kwashe dubban makanikai, masu sana’o’i da ’yan kasuwa daga cunkoson da suke yi a gefen Babbar Hanyar Waje ta Kudu da ke yankin Apo a Abuja, bayan ƙaddamar da muhimman ayyukan more rayuwa a sabon wurin da aka tanada musu a Gundumar Wasa.
Sabbin ayyukan da aka ƙaddamar sun haa da hanyoyin shiga, samar da wutar lantarki da ruwan sha a sabon yankin kasuwanci da aka tsara domin karɓar masu sana’o’in da ke gudanar da harkokinsu a tsohon wurin.
Mai kula da ƙungiyar Haɗin Kan Makanikai da ’Yan Kasuwar Apo, Chinedu Nweke, ya bayyana wannan ci gaba a matsayin cikar alƙawarin da gwamnatoci da dama suka yi shekaru da suka gabata amma suka kasa aiwatarwa.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da ayyukan a Abuja ranar Juma’a, Nweke ya ce shekaru da dama kenan makanikai da masu sana’o’i ke neman a mayar da su zuwa wani tsari na dindindin da ya dace da gudanar da kasuwanci.
Ya ce, tsawon lokaci suna gudanar da sana’o’insu a wani wuri da bai dace ba a gefen babbar hanya, inda gwamnatoci daban-daban suka yi ta alƙawarin kwashe su ba tare da cika ba. A cewarsa, kammala waɗannan ayyukan more rayuwa wata babbar alama ce da ke nuna cewa shirin komawarsu sabon wurin ya kusa zama gaskiya.
Sai dai ya roƙi Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya (FCTA) da ta gaggauta ba waɗanda za su amfana takardun mallakar filayen kasuwancinsu, yana mai cewa hakan zai ba su damar komawa sabon wurin cikin doka.
“Abin da muka gani yau ya ƙara mana ƙwarin gwiwa cewa an kusa kammala shirin kwashemu. Amma muna buƙatar takardun rabon filaye kafin mu fara komawa sabon wurin,” inji shi.
Shirin kwashe masu sana’o’in na daga cikin manyan tsare-tsaren bunƙasa birnin Abuja da Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya ke aiwatarwa domin inganta tsarin birni, rage cunkoso da kuma samar da ingantattun wuraren kasuwanci ga masu sana’o’in hannu.
A nasa jawabin, Shugaba Tinubu ya ce aikin Wasa wani ɓangare ne na ƙudirin gwamnatinsa na faɗaɗa ayyukan more rayuwa a Abuja da kuma samar da yanayin da zai ƙarfafa bunƙasar tattalin arziki.
Shugaban ya yi wannan jawabi ne ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, inda ya ce gwamnati za ta ci gaba da zuba jari a ayyukan more rayuwa masu inganci domin mayar da Wasa cibiyar kasuwanci ta zamani a cikin Babban Birnin Tarayya.
Ya kuma jaddada cewa ɓangaren tattalin arzikin da masu sana’o’i da ƙananan ’yan kasuwa ke tafiyarwa na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi ga miliyoyin ’yan Nijeriya, tare da ba da gagarumar gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
