Motocin haya masu amfani da lantarki sun taimaka wa Chana rage tasirin rikicin Hormuz

Spread the love

Yayin da rikicin mashigar ruwan Hormuz ke haddasa tashin farashin danyen mai da girgiza kasuwannin makamashi na duniya, ƙasar Chana ta samu wata muhimmiyar kariya daga irin wannan matsin lamba ta hanyar faɗaɗa amfani da motocin haya masu amfani da lantarki.

Rahotanni sun nuna cewa a faɗin biranen Chana, yawan fasinjojin da ke amfani da tasi da motocin haya ta manhajojin zamani na ci gaba da ƙaruwa, duk kuwa da tashin farashin man fetur.

Bayanan gwamnatin ƙasar sun nuna cewa a watan Mayu kadai, an yi sama da tafiye-tafiye biliyan 3.05 ta hanyar motocin haya. Wannan adadi ya ƙaru da kashi shida cikin ɗari idan aka kwatanta da daidai wannan lokaci na bara, bayan ɓarkewar yakin Iran a ƙarshen watan Fabrairu.

Masana sun bayyana cewa wannan ci gaban ya samo asali ne daga sauyin tsarin sufurin ƙasar, inda kuɗin haya ke ci gaba da sauka duk da hauhawar farashin man fetur.

Sun ce ƙaruwar masu shiga aikin tuƙin tasi saboda tabarbarewar tattalin arziki, tare da yawaitar motocin lantarki masu araha, ya haddasa gasa mai tsanani tsakanin direbobi, lamarin da ya tilasta rage kuɗin haya domin jawo karin fasinjoji.

Wani direban tasi na wucin gadi a birnin Beijing mai suna Li ya shaida wa Reuters cewa kuɗin haya ya ragu tsakanin kashi 10 zuwa 15 cikin dari tun lokacin da ya fara aikin watanni shida da suka gabata.

Ya ce gasa tsakanin direbobi ta yi tsanani matuƙa, abin da ya sa ake ci gaba da rage farashin tafiya.

A kafafen sada zumunta ma, ɗaruruwan masu amfani da motoci sun bayyana cewa tun bayan tashin farashin man fetur a watan Maris, hawa tasi ya fi musu araha fiye da amfani da motocinsu.

Wata mai mota mai suna Yang ta ce idan farashin mai ya yi tsada, ta fi son hawa tasi musamman zuwa wuraren da suka yi nisa da ba za ta iya hawa keke ba.

Ta ce hakan na rage mata wahalar neman wajen ajiye mota tare da kuɗin sayen man fetur.

Masana sun ce karuwar motocin haya masu amfani da lantarki na ƙara tabbatar da cewa ɓangaren sufuri na Chana na ƙara kauce wa dogaro da man fetur, abin da ke rage tasirin duk wata matsala da ke shafar kasuwar mai ta duniya, ciki har da rikicin Hormuz.

By ukarofi

Leave a Reply