Wani injiniyan ruwa ya bace bayan harin jirgin ruwa a gaɓar tekun Oman 

Spread the love

Iyalan wani injiniyan ruwa dan ƙasar Indiya da ya bace bayan harin da aka kai wa jirgin dakon kaya GFS Galaɗy a gabar tekun Oman sun tabbatar da rasuwarsa, lamarin da ya ƙara nuna yadda rikicin da ke kara tsananta a yankin Tekun Fasha ke jefa ma’aikatan jiragen ruwa cikin haɗari.

Mamacin, Heramb Karmarkar, mai shekaru 30, ya kasance babban injiniyan ruwa a cikin jirgin dakon kaya mai ɗauke da tutar Cyprus, wanda aka kai wa hari a ranar Lahadi yayin da yake gudanar da tafiyarsa ta ruwa a kusa da gaɓar tekun Oman.

Jirgin yana ɗauke da ma’aikata 24, ciki har da ‘yan ƙasar Indiya 11. Hukumomin Cyprus sun bayyana cewa wani makami da ba a tantance asalinsa ba ne ya bugi jirgin, abin da ya haddasa barna tare da bacewar Karmarkar.

Sai dai daga baya Iran ta sanar da cewa ita ce ta kai harin, tana mai cewa jirgin ya yi ƙoƙarin wucewa ta wata hanyar ruwa da ba a amince da ita ba duk da gargadin da aka yi masa ya sauya hanya.

Surukin mamacin, Vivek Tandon, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kamfanin da ke kula da jirgin ne ya sanar da iyalansu cewa Karmarkar ya rasu.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, Ma’aikatar Harkokin Wajen Indiya ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba, duk da bukatar da aka yi mata ta yi karin haske.

By ukarofi

Leave a Reply