Fitaccen ɗan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ya bayyana cewa yana da burin komawa makaranta domin yin karatun jami’a bayan ya yi ritaya daga taka leda, yana mai jaddada cewa ilimi na ci gaba da kasancewa muhimmin buri a rayuwarsa duk da irin nasarorin da ya samu a harkar ƙwallon ƙafa.
ɗan wasan na Nijeriya ya bayyana hakan ne a wata hira da ta sake yawo a kafafen sada zumunta a ranar Litinin, inda ya waiwayi yadda rayuwarsa ta kasance, darussan da ya koya a rayuwa da kuma muhimmancin shiryawa don rayuwa bayan barin wasan ƙwallon ƙafa.
Osimhen ya ce ƙwallon ƙafa ta sauya rayuwarsa baki ɗaya tare da buɗe masa ƙofofin samun damammaki a faɗin duniya. Sai dai ya bayyana cewa ya fahimci rayuwar ɗan wasa tana da iyaka, don haka akwai buƙatar tsara makoma tun kafin lokacin ritaya ya zo.
ɗan wasan na Galatasaray ya ce duk da cewa ya samu darussa masu yawa ta hanyar gogewar rayuwa, har yanzu yana bai wa ilimin zamani muhimmanci, kuma yana fatan samun digirin jami’a nan gaba.
Gwarzon ɗan Wasan Afirka na Shekarar 2023 ya bayyana cewa komawarsa makaranta ba wai kawai cika wani buri ne na kansa ba, har ma zai zama abin ƙarfafawa ga matasan Nijeriya da suka dakatar da karatunsu saboda matsalolin kuɗi ko wasu ƙalubale na rayuwa.
Ya ce yana son mutane su fahimci cewa barin makaranta a wani mataki ba yana nufin ƙarshen neman ilimi ba ne, domin duk lokacin da mutum ya shirya, ƙofofin ilimi suna nan a buɗe.
Osimhen ya bayyana cewa kowanne ɗan wasan ƙwallon ƙafa zai zo ranar da zai daina taka leda, don haka yana da matuƙar muhimmanci mutum ya mallaki ilimi da ƙwarewar da za su amfane shi bayan ritaya.
A cewarsa, ya kamata ‘yan wasa su riƙa kallon rayuwarsu fiye da lokacin da suke taka leda, tare da shirya kansu domin sabon babin rayuwa da ke gabansu.
