Shettima ya tafi Sierra Leone wakiltar Tinubu a taron ECOWAS na 69

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja, idna ya nufi zuwa Freetown, babban birnin ƙasar Sierra Leone domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Ƙungiyar Ƙasashe Masu ƙarfin Tattalin Arziƙi ta Afirka ta Yamma (ECOWAS) karo na 69.

Taron, wanda za a gudanar a ranar Asabar a babban ɗakin taro na Julius Maada Bio, Freetown, zai haɗa kan shugabannin ƙasashe, ministoci, manyan jami’an gwamnati da cibiyoyin shiyya domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi Afirka ta Yamma.

A wata sanarwa da Kakakin mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce Shettima zai shiga cikin jagororin siyasa da na kasuwanci daga sassan yammacin Afirka a babban taron.

Ana sa ran taron ya duba muhimman tsare-tsare da dabaru warware matsalolin da suka shafi shiyyar da kuma manufar bunƙasa haɗin kai tsakanin ƙasashen ECOWAS domin samun ci-gaba a fanin zaman lafiya, dimukraɗiyya da tattalin arziƙi.

Haka kuma, taron zai bayar da dama ga ƙasashen ECOWAS na su yi nazari akan nasarorin da aka samu a shiyyar a fannonin tsaro, shugabancin dimukraɗiyya, kasuwanci, ababen more rayuwa, tattali da kuma ci-gaba mai ɗorewa.

Wannan zama na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen shiyyar da dama suke fuskantar ƙalubalen tsaro da sauye-sauyen yanayin siyasa da ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai ta fuskar tattalin arziƙi.

By Babaji

Leave a Reply