COVID-19: Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin saukaka dokar kulle

Daga jaridar Manjaha

Gwamnatin Tarayya ta sanar da saukaka dokar kulle a karo na uku, inda ta kara wa’adin dokar da wata guda.

Kwamitin Shugaban Kasa Kan Yaki da Cutar Korona (PTF) ne ya bayyana haka a Litinin da ta gabata a Abuja, yayin da yake gabatar da rahoton ayyukansa na mako-mako kamar yadda ya saba.

Da yake jawabi, shugaban kwamitin Boss Mustapha ya ce, “PTF na nan na kokarin inganta sha’anin tafiye-tafiye zuwa ketare domin takaita kalubalen da matafiya kan fuskanta.

“Haka nan, kwamitin na nazarin matakan sassauta dokar kulle karo na uku kasancewar wa’adin dokar da aka sanya a baya ya kare a yau.”

Ya kara da cewa, “Duba da adadin masu harbuwa da cutar ba raguwa yake yi ba, don haka an kara wa’adin dokokin da aka gindaya da wata guda wanda zai soma aiki daga ranar Talata, 26 ga Janairun 2021.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *