“Filayen Nijeriya mallakar jihohi ne ba na Fulani ba” – Sanata Jibrin

Daga Fatuhu Mustapha

An yi kira ga al’umar Fulani a fadin Nijeriya da su rungumi zaman lafiya da sauran kabilu tare da bai wa gwamnatocin jihohi hadin kai wajen yaki da ta’addanci. Sarkin Fulanin jihar Nasarawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin ne ya yi wannan kira a wata sanarwa da ya fitar yau Talata.

Jaridar Manhaja ta ruwaito Sanata Jibrin na cewa, “Ba na tare da duk wanda ke ra’ayin Fulani ne ke da mallakar filayen Nijeriya. Jihohi su ke da mallakar filaye.”

Sarkin Fulanin ya yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman gwamnoin Ondo da Oyo da al’ummominsu da kuma hukumomin tsaro na jihohin da lamarin ya Shafa hada da dukkan Fulani, da a yi sulhu ta hanyar tattaunawa domin magance rashin fahimtar da ke tsakanin jihohin da lamarin ya shafa da Fulanin da ke zaune ciknsu. Yana mai cewa, “Dole ne a yi zaman lumana da juna tsakanin Yarabawa da Igbo da kuma Ijaw.”

A cewar Sanata Jibrin, “Ina goyon bayan duka gwamnonin da ke kokarin ganin an magance matsalolin da ke tsakanin Fulani makiya da manoma a kowace jiha. Umarnin barin jihar Ondo da aka bai wa Fulani mazauna jihar a dakatar da shi sannan a bar dattawa da gwamnoni su kula da batun a natse.

“A matsayina na shugaban Fulani, ni da wasu dattawa muna kokarin yadda za mu gayyato dukkan kungiyoyin Fulani don mu zauna a samar da mafita ba tare da an tada kura ba. Muna zaman lafiya da juna tun bayan yakin Biyafra. Ina amfani da wannan dama wajen yaba wa gwamnoninmu bisa kokarin da suke yi wajen magance matsalolin da Fulani makiya ke fuskanta, da fatan za a sahawo kan matsalolin nan ba da dadewa ba.”

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*