Daga Umar Gombe
Bayanan da jaridar Manhaja ta samu daga Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, sun nuna Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabbin hafsoshin sojin Nijeriya.
Wadanda nadin ya shafa su ne; Major General Leo Irabor a matsayin babban hafsan tsaron kasa da Maj. Gen. I Attairu a matsayin babban hafsan sojojin kasa, sai A Z Gambo a matsayin babban hafsan sojojin ruwa da kuma AVM IO Alao a msatsayin babban hafsan sojojin Sama.
Kafin wannan lokaci, ‘yan Nijeriya da dama sun yi ta bayyana ra’ayoyinsu kan bukatar da ke akwai na yi wa shugabannin sojoji garambawul don inganta sha’anin tsaro.