Zamfara: ‘Yan bindiga sun kai hari mahaifar ministan tsaro, sun yi awon gaba da mutane sama da 50

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wasu gungun ‘yan ta’adda sun mamaye garin Maradun, hedikwatar ƙaramar hukumar Maradun kuma mahaifar ƙaramin ministan tsaro, Hon. Bello Muhammad Matawalle, inda suka yi garkuwa da mutane fiye da 50 galibinsu mata, a jihar Zamfara

Wani mazaunin yankin, Malam Sulaiman Maradun, a wata tattaunawa ta wayar tarho ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun yi wa garin ƙawanya da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar daren ran Alhamis inda suka gudanar da harin nasu gida-gida.

“Abin takaici ne yadda suka mamaye garinmu saboda sun zo da wasu manyan makamai masu kisa, suka fara harbe-harbe tsakar daren yau Juma’a,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, ‘yan bindigar sun kashe Sama da mutum 10, sannan sun yi awon gaba da dabbobin jama’ar yankin.

Ya ci gaba da cewa, ‘yan bindigar sun kai hari fadar Sarkin Maradun, Alh. Garba Tambari, a lokacin da Sarkin ba shi a garin .

Ya ce, “Kamar yadda nake magana da ku yanzu, mutane da yawa, galibi mata ne waɗannan ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a yayin harin, kuma da dama daga cikin mutanenmu ba a gan su ba, har yanzu ba a san inda suke ba.

“Wannan ba shi ne karon farko da waɗannan ‘yan ta’addan da ake fargabar ke kai hare-hare kan al’ummar Maradun ba, ya kamata gwamnati ta ɗauki tsauraran matakai don magance matsalar rashin tsaro da ke addabar yankinmu”.

Maradun ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara da su tura ƙarin sojoji yankin domin ceto mutane daga munanan ayyukan ‘yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

Ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Asp Yazid Abubakar da wakilinmu ya yi, ya ci tura, domin ba a samu dukkan layukan sa ba yayin da ake haɗa rahoton.