Rundunar sojojin Isra’ila ta amince da murabus ɗin shugaban hukumar leƙen asirinta

Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Isra’ila Aharon Haliva ya yi murabus, sakamakon harin da ba a taɓa ganin irinsa ba da ƙungiyar Hamas ta kai wa ƙasar a ranar 7 ga watan Oktoba.

Haliva ya kasance babban jami’in gwamnatin Isra’ila na farko da ya aje muƙaminsa tun bayan harin Hamas da ya hallaka mutane 120o, sannan ta yi garkuwa da wasu kusan 250 da har yanzu ba a kammala kuɓutar da su ba.

Jim kadan bayan harin, tsohon shugaban hukumar leƙen asirin ya ce a ɗora masa laifin rashin daƙile harin da Hamas ta kai cikin ƙasar, don haka ya ce zai sauka daga muƙaminsa.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila ta fitar, ta ce babban hafsan sojin Isra’ila ya amince da buƙatar Haliva ta yin murabus, sannan ya gode masa bisa irin gudunmuwar da ya bai wa ƙasarsa.

Ana ganin murabus ɗin nasa na iya buɗe hanya ga wasu manyan jami’an tsaron Isra’ila su amince da laifin rashin daƙile kai harin da Hamas ta yi, su kuma bi sahunsa wajen sauka daga kan muƙamansu.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Isra’ila ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare ta kasa a yankin Rafah, duk kuwa da matsin lambar da ta ke fuskanta daga ƙasashen waje.